Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Matakan Gwamnati Na Dab Da Ruguza Kasuwanci A Neja – Dandare

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa a Neja, Alhaji Abubakar Muhammad Dandare yace matakan da gwamnatin jiha ke dauka kan annobar cutar Koronabiarus yana gab da tsayar da harkokin kasuwanci a jihar nan. Shugaban ya bayyana hakan ne littinin din makon nan kan yadda kayayyakin bukatun jama’a ke ta yin tashin gauron zabi a kasuwannin jihar.
Dandare matsalar da ake samu gwamnati ta kasa baiwa ‘yan kasuwa tallafi, sannan kusan kayayyakin da jama’a ke bukata dole sai an tafi manyan kasuwanni kamar Kano ko Legas, kuma abin takaici idan ma ka samu nasarar sayo kayan shigowa da su wani babban tashin hankali, shi yasa kananan ‘yan kasuwa ke anfani da wannan damar wajen kara farashin kayayyaki, domin ma idan ka sayar da wanda ka ke da shi babu tabbacin za ka iya samun wasu kayan ba su a cikin shaguna.
Dandare yace lallai cutar Korona gaskiya ce, ba daukar mataki akan abinda ba ka shiryawa ba, domin kasashen da suka cigaba da ma cutar ke masu barazana fiye da mu irin yadda suke ware kudade dan tallafawa kananan ‘yan kasuwa. Amma gwamnati ba wani tanadin da ta yi mana kuma ta umurci a rufe kasuwanni, akwai kananan ‘yan kasuwa da dama wadanda sai sun fito ne suke samun abinda za su ci da iyalan su, yanzu wadannan ya ka ke son su yi da rayuwar su.
Ya kamata kamar yadda aka bada damar shigowa da magunguna da abinci, su kayayyakin bukatun yau da kullun a bada damar shigowa da su.
Kan tsadar kaya da ake magana, akwai ‘yan kasuwan mu su hudu sun tafi sayen kaya a Onisha, dakyar suka kubuto suka dawo, wanda wannan ba daidai ba ne, wannan matakin mataki ne da zai jefa dubban jama’a cikin mummunar yanayi.
Shawarar da zai baiwa gwamnatin jiha da a samar da yanayin da za a baiwa ‘yan kasuwa tallafi, a samar da yanayin da saukaka wannan radadin da jama’a ke ciki a halin yanzu, amma in ba haka ba kuwa idan Korona ba kashe jama’a ba. yunwa ko zai yi daidai da rayukan mutane.
Wannan cutar ba a jihar nan kawai ake fuskantar matsalolin ta ba, kusan duniya ne ke fuskantar wannan matsalar, babban matsalar ana zama ne ana yin doka ba tare da an tuntubi jama’a, ka ga duk lokacin za a ce ba a shigo da kaya a kasuwanni to lallai za a fuskanci matsaloli da dama.
Dan haka ina jawo hankalin gwamnatin tarayya, jiha da karamar hukuma a duk lokacin da za a zartas da wani kuduri a rika la’akari da halin da marasa karfi zasu samu kan su, domin hatta tallafin da gwamnati ke cewa ta bayar bai kaiwa hannun wadanda ya kamata su anfana da shi, sannan a rika yin shirin da ba zai bada damar tsayawar harkokin kasuwanci ba, domin tsayawar kasuwanci waje daya zai jefa jari da rayukan ‘yan kasuwa cikin wani yanayi mara tabbas.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: