Korona: NCDC Ta Shawarci Masu Juna Biyu

Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta shawarci masu juna biyu da kuma mata masu shayarwa da su dauki matakan kariyar da suka dace domin kare kansu daga cutar Korona.

Dr Chikwe Ihekweazu, Daraktan NCDC din ne shi ne ya shawarce su a hirar da ya  yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Abuja.

Ihekweazu ya ce wannan shawarar sun bayar ne bisa shawarar da sashen lura da lafiyar iyali na ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya ta bayar.

Inda ya lissafo hanyoyin matakan kariyar da ya kamata masu juna biyu da masu shayarwa su bi, wanda ya hada da wanke hannu, nesanta kawukansu da cunkoson jama’a, tare da kare kansu daga masu tari ko atishawa ko wadanda suke nuna alamomin kamuwa daga cutar Korona.

Exit mobile version