Connect with us

LABARAI

Korona : NOA Ta Dukufa Wajan Wayar Da Kan Al’umna Wajan Da NIRSAL Za Ta Da Al’umma A Zamfara

Published

on

Hukumar wayar da kan al’umma ta kasa watau NOA, reshen jihar Zamfara, ta yi kira ga al’umma suci gaba da bin hanyoyin riga-kafin dakileta kamuwa da annobar Korona da ta addabi duniya baki daya da kuma wayar da kan al’umna wajan amsar Rance NIRSAL da babban bankin kasa zai bada dan farfado da harkar kasuwanci .

Daraktan hukumar na jihar Zamfara, Hadiya Yahaya Katsina ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da ‘yan Jaridu a ofishisa da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.

“Hadiya Yahaya Katsina ya bayyana cewa, wannan annoba iska takebi, kuma duk wanda ya kusanci mai ita nan take ya ke kamuwa da ita, idan ko mutum yana dauke da rigakafin ta na takunkumin baka da sinadarin goge hannu zai taimaka gaya wajan kin kamuwa da ita in ji Daraktan.

“Daraktan ya jinjinna wa gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara,karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun wajan yaki da cutar ta kowane sashe a fadin jihar ta Zamfara .

“Kuma yayi kira ga al’umma da suci gaba da bin umarnin ma’aikatan lafiya a kodayaushe kuma a duk inda suke dan ganin annobar bata shigo cikin jihar Zamfara ba.

“Haka kazalikama Daraktan ya kuma bayyana cewa, ‘ Hukumar ta yi wa jami’an ta na kananan hukumomi tireni akan wayar da kan alumma wajan ganin sunci moriyar tallafin bashi da bankin kasa zai ba da ga ‘yan kasuwa na naira biliyan hamsin watau (CBN).

“kuma tuni wannan hukumar ta baza jami’anta a kowace mazabar kamsula mutum biyar dan wayar masu da kai da kuma yimasu rijistan samun wannan rance da bankin zaibada dan farfado da harkar kasuwanci da annobar Korona ta dakile.

A karahe Daraktan yayi kira ga alummar jihar Zamfara, da su naimi jami’an su a kowane lungo da sako dan cin moriyar wannan tallafi na bankin kasa watau (CBN).
Advertisement

labarai