Connect with us

LABARAI

Korona Rudu Ce Kawai, In Ji Gwamnan Kogi

Published

on

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fada a ranar Talata cewa tsoron annobar Korona tana yin kisa fiye ma da yanda ita cutar a kanta ke yin kisan.

A cewarsa, wannan cutar da ta kashe kimanin mutane 510,909 a fadin Duniyar nan ya zuwa ranar Talatan nan da ta gabata, “cuta ce da aka tilasta ta a kan mutane,” domin gajarta kwanakin rayuwarsu.
Gwamnan ya ja musu da Cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar nan dangane da mutuwar babban alkalin alkalan Jihar ta Kogi, Mai Shari’a Nasir Ajanah.
Ajanah ya mutu ne a ranar Lahadi, a sashen wadanda ake kebancewa a sabili da kamuwa da cutar ta Korona da ke Asibitin Gwagwalada.
Jana’izarsa wacce aka gudanar da ita a makabartar Gudu da ke Abuja, an gudanar da ita ce a bisa tsarin jana’azar wadanda suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar ta korona kamar yanda hukumar ta NCDC ta kayyade.
Bello ya zargi hukumar ta NCDC da bayar da lissafin mutanen da suka rasu a sakamakon kamuwa da cutar wanda a cewarsa sam ba daidai ne ba, ko kuma ba dai ‘yan Jihar na shi ne ba.
Da yake magana a ranar uku da rasuwar babbab alkalin alkalan a ranar Talatan nan, Gwamnan ya bukaci mutane da su daina firgita.
Gwamnan ya kwatanta annobar ta Korona da cewa cuta ce mafi hatsari a kan barnar da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran masu aikata kisan kare dangi suke yi in an hada su bakidaya, ya kara da cewa, cutar kirkirarra ce, amma abin takaici aka zo aka siyar da ita ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce Mai Shari’a Ajanah, ya mutu ne mutuwa kamar yanda aka saba mutuwa, don haka sai ya bukaci mutane da su daina danganta mutuwar na shi da wani abu na daban kamar yanda wasu mutanan suke rade-radin yi domin cimma wata manufa ta su ta siyasa da bata mutane.
Gwamnan ya ce: “Ka da ku firgita da batun annobar Korona. Cuta ce wacce aka yiwo safararta, ake yada ta ake kuma tilasta ta a kan mutane ba tare da wani dalili ba.
“Ba abin da ke kisa fiye da firgita. Ina bukatar ku da ka da ku yarda da koronar da aka dauko aka ajiye.
“An kirkirota ne kawai domin a jefa wa mutane razani, tsoro da annoba da aka kirkiro domin a gajarta rayuwar mutane.
“Ko Likitoci da kwararrun jami’an lafiya su yarda ko ka da su yarda, an kawo Korona ce domin a gajarta rayuwar mutane. Cuta ce da ake yada ta ta hanyar tilasta ta a kan ‘yan Nijeriya su yarda da ita.
Bello ya kwatanta marigayi Ajanah a matsayin kwararren masanin harkar shari’a kuma masoyin zaman lafiya. Ya roki Allah da ya saka ma sa da aljannar Firdausi.
Mutuwar ta Ajanah ta biyo bayan mutuwar alkalin kotun daukaka kara ta gargagajiya ne, Mai Shari’a Ibrahim Shaibu Atadoga, wanda ya mutu a bayan wata gajeruwar rashin lafiya a ranar 21 ga watan Yuni.
A watan Mayu, Jihar Kogi ta musanta sanarwar kamuwar mutane biyu a cikin Jihar na ta da cutar ta Korona wanda hukumar ta NCDC ta bayar da sanarwa.
“Har ya zuwa yanzun, babu sanarwar kamuwa da cutar ta Korona a Jihar ta Kogi. Mun gabatar da cikakken bincike, mun kuma gwada daruruwan mutane ya zuwa yanzun, kuma babu wanda muka samu da cutar ta Korona,” in ji Kwamishinan Lafiya na Jihar ta Kogi, Saka Audu.
Jihar ta Kogi tana zargin a na shirya mata makirci ne domin a tilasta mata cutar ta Korona a cikin Jihar.
Jihar ta Kogi ta hana ma jami’an hukumar ta NCDC shiga cikin Jihar domin su yi gwajin a cikin Jihar, y adage da cewa Jihar ta shi ta gudanar da daruruwan gwajin da kanta kuma duk ba ta sami wani da cutar ta Korona ba.
A nan take Gwamnan ya umurci jami’an hukumar ta NCDC da su hanzarta ficewa daga cikin Jihar ko kuma ya killace sun a tsawon kwanaki 14.
Advertisement

labarai