Connect with us

MAKALAR YAU

Korona: Sake Kakaba Ma Na Dokar Hana Fita Alkaba’i Ne

Published

on

Jama’a bi-la-adadin sun kawo iya wuya da suka ji zancen akwai yiwuwar a sake sanya dokar hana fita saboda yadda kamuwa da cutar Korona ke karuwa a kasar nan.

Da farko, a makon da ya gabata, an yi ta rade-radin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i zai sake kakaba wa al’ummar jihar dokar a ranar Litini ta makon jiya. Yamadidin da aka yi ta yi kan lamarin ya tayar da hankulan mutane sosai. Domin na kasance a Kaduna, a ranar Juma’ar makon jiya har zuwa ranar Lahadi. Da yake an san ni danjarida ne, kusan duk inda na ziyarta sai an samu mutanen da suka sheko a guje suka tambaye ni game da gaskiyar lamarin . Amsar da nake bai wa mutane a lokacin ita ce, su kwantar da hankulansu, idan gwamnatin Kaduna tana da shirin hakan; za ta sanar tare da bayar da tazara kafin dokar ta fara aiki, akalla za a samu ‘yan sa’o’i ko kuma kwanaki. Bayan haka sai na fayyace musu bayanan da aka ruwaito Gwamna El-Rufa’i ya yi a kan lamarin yayin kaddamar da wasu na’urorin gwajin cututtuka na tafi-da-gidanka da gwamnatinsa ta yi.

Gwamnan ya nunar da cewa matukar jihar ta samu hauhawar bullar cutar ta Korona,hakan na iya tilasta musu sake sanya dokar hana fita domin dakile ta. Shi a ganinsa, wajibi ne a sake daukar matakin hakan ko da kuwa wasu jihohi a fadin kasar suna ci gaba da sassauta dokar.

“Har yanzu muna nazarin sakamakon bin ka’idojin da aka shimfida na sassauta dokar a wuraren ibada, za mu yi la’akari da abin da hakan ta haifar da kuma lura da yawan karuwar cutar, muna iya sake sanya dokar ta hana fita. Ina fadar wannan ne domin kowa da kowa da ke Jihar Kaduna ya ji ma kunnensa, matukar an kai wani mataki da cutar za ta gagari tsarinmu na kiwon lafiya da ma’aikatan lafiya da muke da su, za mu sake kafa dokar hana fita, za mu koma kamar yadda muka yi a baya. Ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna su bi ka’idojin da aka shimfida da kuma takaita zirga-zirgansu,” a ta bakin El-Rufa’in.

Wadannan abubuwan da ya ambata su ne suka tayar da hankulan jama’a, saboda suna murna bako ya tafi; a she mugun yana bayan gari.

Sai dai duk da haka, bai dace mutanen da suka daga hankulansu a kan jawabin Gwamnan, su karkata ga sashe daya na jawabin nasa ba, akwai dayan sashen jawabin wanda za a iya cewa ya yi togaciya game da sanya dokar. Ko a tsakuren da na kawo a sama, Gwamnan ya ce matukar sun ga abin yana nema ya gagari kundila ne za su dauki wannan matakin.

Bugu da kari, ya ce, “tsarin kiwon lafiyarmu yana da matukar karfi sosai kuma muna da kayan aiki na gwaje-gwaje. Mun gamsu da yadda muke yaki da cutar kuma mun samu kyakkyawan sakamako wajen warkar da wadanda suka kamu. Amma duk da haka ba za mu yi sakaci ba”. Kenan kai-tsaye ba za a iya cewa kada’an Gwamnan ya riga ya yanke shawarar sake kakaba dokar ba ballantana ma har a kai ga rade-radin ya sanya ranar da za ta fara aiki ba.

Kodayake idan an bi ta barawo a bi ta mabi sawu, mutane sun sha wuya sosai da tsananin El-rufa’i lokacin da ya sanya dokar hana fita, domin abin na shi ya zama babu sani ba sabo. Shi ya sa mutane za su fara shiga fargaba da zarar sun ji ya ambaci sake kakaba dokar. Akwai mutane da dama da na ji sun sauya wa El-Rufa’i suna daga Gwamnan Kaduna zuwa Gwamnan Wuhan, yankin kasar Sin (China) da cutar Korona ta fara bulla saboda tsananin da ya sa a kan dokar kulle.

Mutane da dama ba a Jihar Kaduna ba kawai, sun soki Gwamnan a kan hakan, saboda a ganinsu bai kamata a ingiza mutane cikin tsanani biyu ba, azabar yunwa da azabar Korona. Ko da gwamnatin jihar ta raba kayan tallafi hannun ‘yan siyasa abin ya sauka da kashi 90 a cikin 100. Kuma kowa ya san halin ‘yan siyasarmu da handama da babakere. Sannan fahimtar Gwamnan ta za a sa doka in ya so daga baya a bai wa mutane hakuri gurguwa ce, ta yaya za ka kuntata wa mutum kana sane ko a ce da gangan sai ka fake da ba shi hakuri bayan shan wuya? Wannan ai ko dan karamin yaro ma ya san yin hakan wasa da hankali ne.

Annobar Korona da ta auko mana gaskiya ce, yaki da ita wajibi ne, riga-kafin kamuwa da ita dole ne, amma yana da kyau a nemi hanyoyi mafi maslaha. Kwaikwayon tsari ko hanyoyin da Turawa suka bi wajen yaki da cutar ba namu ba ne, saboda tazarar da ke tsakaninmu da su dangane da ci gaban rayuwa. Gashin kanmu ba irin nasu ba ne, shi ya sa idan muka ce sai mun yi irin kitsonsu, za mu kare ne da tuge gashin kan namu har da fata ba kuma tare da mun cimma muradi ba.

Masana da dama lokacin da aka samu bullar cutar a yankinmu na Nahiyar Afirka sun yi rubuce-rubuce tare da bayar da shawarwari a kan kar mu sake mu ce za mu bi hanyoyin da Turawa suka dauka na yaki da cutar. Suka ce mu kalli matsayin tattalin arzikinmu da yanayin rayuwarmu da al’adunmu, sai mu samar da mafitar da za ta fi zama mana alheri wurin yaki da Korona. Amma gwamnatocinmu suka yi biris da su.

Hasashen da Turawa suka yi mana na yadda Korona za ta yi kaca-kaca da mu a Afirka ya koma kansu. Idan ban manta ba, a tsakiyar karshen watan Maris zuwa farkon watan Afirilu sun kiyasta cewa dubban daruruwan Afirkawa za su bakuncin lahira saboda Korona, amma har zuwa yau, yankin shi ne yake da mafi karancin wadanda suka mutu ta sanadiyyar Korona. Ashe godiya ga Rabbul Alamina ya kamata mu dukufa da yi domin mun tabbata wannan kariyarsa ce kawai. Domin ba mu da kayan aiki na yaki da cutar kamar yadda Turawan suke da su, sai kuma ga shi cutar ta fi yi musu kanta duk da rantsattsun kayan aiki na zamani da suke da su a kan kowane fanni ba ma na kiwon lafiya ba kawai!

Saboda haka ya dace daga yanzu duk irin matakin da gwamnatocinmu suke son dauka na yaki da cutar, su yi la’akari da rahamar da Allah ya yi mana ta hana cutar yi mana kisan kwaf-daya kamar yadda Turawa suka yi hasashe.

Musamman a Jihar Kaduna, an samu gagarumin ci gaba a fannin yaki da cutar bisa kaddamar da wadannan na’urorin na gwaje-gwajen kiwon lafiya na tafi-da-gidanka. A duk fadin kasar nan babu inda ake da wadannan na’urorin in ba a Kaduna ba. Baya ga kasar Afirka ta Kudu, a duk fadin Afirka Jihar Kaduna ita ce ta biyu da ta samu na’urar bisa tallafin Hukumar Tallafa wa kasashen Duniya na Amurka (USAID) da kuma Gidauniyar KNCbTB da ke Nijeriya. Kenan Gwamna El-Rufa’i idan ba ka gode wa Allah a kan wannan rahama tasa ta hanyar sassauta wa bayinsa ba, ai ba ka kara tsananta musu ba!

Kodayake ba Gwamna El-Rufa’i ne kadai ya yi batun sake kakaba dokar hana fitan ba. Shugaban Kwamitin Shugaban kasa na Yaki da Korona, Boss Mustapha shi ma ya yi irin wannan mugun fatan, inda shi ma aka ruwaito shi yana cewa da yana da iko, lokaci ya yi da zai sake kakaba dokar hana fita a kasar nan saboda sakacin da ya ce mutane suna yi da cutar da kuma karuwar bazuwarta.

Tabbas yana da matukar tashin hankali yadda aka samu karuwar cutar da sama da dubu uku a tsakanin mako daya kacal (karshen makon da ya gabata zuwa farkon makon nan). Amma kuma sake rufe mutane bai kamata ya zama zabi na karshe ba.

Abin da Boss Mustapha ya yi ikirari na karuwar cutar mai tayar da hankali baro-baro a fili yake bisa kididdigar da Hukumar NCDC ke bayarwa, kuma babu shakka ‘Yan Nijeriya suna sakaci da riga-kafin kamuwa da cutar ta hanyar kin bin sharuddan zirga-zirga da aka shimfida. Hatta amfani da takunkumin riga-kafi galibin mutane sun daina yi, ko kuma ba za a sa ba sai an kusa da inda jami’an tsaro ke bincike. Wannan sakacin ya hada har da shugabanni ba talakawa kawai ba. Ashe kenan ana bukatar tilasta amfani da sharuddan da aka gindaya ne ba sake kakaba dokar ba.

Lallai abu ne mara dadi bisa yadda Korona ta karu da wajen kashi fiye da dari bisa dari a wannan wata na Yuni, amma kuma ya wajaba kafin a dauki matakin sake rufe mutane, Kwamitin Yaki da Korona ya fahimtar da al’umma alakar karuwar cutar da karuwar gwajin da ake yi na cutar. Sannan kwamitin ya taimaka mutane su fahimci dalilin da ya sa aka samu karuwar mace-mace ta sababin cutar, misali kamar a ce fiye da yadda ake samu a kasar Ghana.

Haka nan, wajibi ne kwamitin ya taimaka ya fahimtar da ‘Yan Nijeriya dalilin da ya sa Nijeriya ta shallake Ghana a yawan masu cutar duk da kasancewar a farkon kamuwa da cutar Ghana ta fi Nijeriya yawan masu kamuwa, sannan Ghana ta riga Nijeriya sassauta dokar hana fita amma duk da haka Nijeriya ta fi yawan masu cutar.

Kar a manta, tattalin arzikin kasa yana shure-shuren mutuwa sakamakon dokar hana fita. Don haka wajibi ne gwamnati ta yi nazari gaba da baya, ciki da waje a kan duk wani mataki da za ta sake daukawa game da cutar tare da aiwatarwa domin zaman lafiya, kiyaye rai da kuma muradin ‘Yan Nijeriya, maimakon kwaikwayon kasashen waje.

Hatta Chana, lokacin da cutar ta sake bullowa a karshen makon nan, ta kange mutanen yankin da abin ya shafa ne kawai wadanda dududu ba su wuce dubu dari biyar ba a cikin al’ummar kasar da ta kai yawan fiye da biliyan daya.

Saboda bala’in da dokar hana fita ke jefa mutane a ciki, duk mai neman sake kakaba dokar, bakinsa ya sari danyen kashi!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: