Connect with us

RIGAR 'YANCI

Korona: Sanata Bomai Ya Tallafa Wa Mazabarsa Da Buhunan Abinci 14,000

Published

on

A kokarin sa wajen rage wa al’ummar mazabar sa, a daidai lokacin daukar matakan dakile yaduwar annobar korona, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai, mai wakiltar kudancin jihar Yobe a zauren majalisar dattijai, ya tallafa wa jama’ar sa da kayan abinci.

A zantawar sa da manema labarai, mai taimaka wa dan majalisar, Musa Ibrahim Musale, ya tabbatar da cewa yanzu haka su na aikin tura kayayyakin abincin zuwa kananan hukumomi hudu a shiyyar kudancin Yobe, wadanda su ka kunshi Potiskum, Fune, Fika da Nangere.
“Yanzu haka ya turo buhunan abinci 14,000 na masara, gero da dawa don raba wa a fadin wadannan kananan hukumomi hudu, wadanda yake wakilta a zauren majalisar dattijai. Wannan daya kenan a bangaren tallafin rage radadin wahalhalun da jama’a ke fuskanta a daidai wannan lokaci wanda duniya ke yaki da annobar cutar Korona.”
Bugu da kari kuma ya ce, wannan idan an hada da ayyukan ci gaba da yake shimfida wa a wannan yanki nashi, kamar “shimfida hanyoyin mota da magudanun ruwa a unguwar Tandari da kan titin Misau, yanzu haka ayyukan su na ci gaba da gudana, duk da barazanar annobar Korona.”
Haka kuma ya yi kira ga jama’ar yankin da cewa su ci gaba da ba gwamnati cikakken goyon baya dangane da manufofi da tsare-tsarenta, wanda ta hakan ne za su ci gaba da cin gajiyar romon dimukuradiyya.
Alhaji Musale ya kuma tunatar da jama’ar mazabar da cewa su yi amfani da lokacin azumin watan Ramadan wajen dagewa da addu’o’in neman taimakon Allah ya kawo mana karshen wannan annoba ta korona kasashen duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: