Connect with us

Uncategorized

Korona: Shugaban Karamar Hukumar Keffi Ya Kori Mutum Tara Zuwa Kano

Published

on

Tabbacin matakin da Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauka na da katar da duk wani mutumin da ya fito daga Jihohin Lagos da Kano  cewa ba zai samu masauki a jihar ba har sai an tantance shi.
Gwamnatin ta mika madafun iko ga duk kanin Shugabannin kananan hukumomi da ke jihar.
Wannan ya sanya Shugaban karamar hukumar Keffi Alhaji Abdulrahman Sani-Maigoro ya juya motar wasu mutum tara da suka fito daga jihar Kano zasu ya da zango a garin Keffi dake jihar Nasarawa a ranar Laraba.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar masu cewa ba zai zuwar ido yana kallon mutani da suka fito daga jihar Kano da ake koka da illolin masu hadari su shiga cikin garin Keffi ba tare da an tantance su ba.
Shugaban karamar hukumar ya ce, matukar zasu shiga cikin garin Keffi to babu makawa sai an killace su na tsawan kwanaki anyi gwaji a tabbatar da basu da wannan cutar ta Korona bairos.
Bayan rashin amince war su, na nuna jayayya ya sanya Alhaji Sani  Mai Goro ya bukaci motar da ta dauko mutanin da ta juya ta koma jihar Kano ba tare da ko da mutum daya kafar sa ya taba kasa ba.
Shugaban karamar hukumar Keffi Alhaji Sani Mai Goro ya ce wannan mataki ne da Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauka domin kare rayuwar alumman jihar ta.
Ya ce  kowa ya san halin da ake ciki na barazanar ya duwar cutar Korona bairos da take addabar al’umma a ko ina cikin fadin Duniya.
Shugaban karamar hukumar Keffi ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule saboda matakin da ya dauka na kare lafiyar alumman jihar.
Ya ce, babu Gwamnan da yake fatan irin wannan annobar ta addabi alumman jihar shi. Kuma jihohin da annobar cutar Korona bairos ta addabe su muna yi masu adu’a Allah ya kawo sauki ya kawo karshen cutar a Duniya baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: