Connect with us

LABARAI

Korona: Shugabanni Su Sassauta Doka Domin A Samu Damar Ibada A Ramadan – Ustaz Ahmad

Published

on

[tps_header][/tps_header]

Limamin Masallacin Jumma’a, na garin Magama Gumau,  karkashin Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), cikin Karamar Hukumar Toro da ke jihar Bauchi, Ustaz Ahmad Suleiman, ya yi kira ga daukacin al’ummar musulmi su rubanya addu’o’i a wannan wata na Ramadan mai falala da muke ciki.

Ya yi kiran ne a tattaunawarsa da wakilimmu, game da shigowar watan Azumin Ramadan da mas’alar da mutane ke fuskanta a dalilin bullar cutar Koronabairus a Duniya.
Sai dai ya fara ne da tsokaci a game da shirin Tafsirin bana.

“Shirye-shiryen gudanar da Tafsiri na wannan shekara yanzu ya yi nisa kusan mun kammala komai abin da muke jira kawai shi ne samun umarni daga wajen shugabannimmu da suke tsara mana aikin yin Tafsiri din don fara gudanar da shi kamar yadda su tsara kuma zan yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin al’ummar musulmi na wannan kasa da su yi amfani da wannan wata mai alfarma su kara koma ga Allah, su tuba masa don ya yafe masu zunubansu a kan wadansu munanan ayyukan da suke aikatawa domin Allah mai rahama mai jinkai mai karbar tuban bayinsa ne matukar sun yi nadama sun nemi yafiyarsa.

“Ina kuma kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnonin kasar nan da su sassauta dokar yadda al’ummar musulmai za su sami sukunin gudanar da ibadunsu ba tare da an tayar masu da hankali ba, haka zai basu damar yin addu’o’in neman samun sauki ga wannan cutar da ta addabi Duniya a yau kuma da neman yafiya wa Allah a kan wadansu munanan ayyukan da suke aikatawa. Domin dukkan Annabawan nan da suka gabata haka al’ummominsu suka yi a duk wani lokaci da wani Annoba ko masifa ta same su sukan yi gaggawa su je wajen Annabawansu su neme su da su roka masu Allah kuma sukan roki Allah ya yafe su ya kawo masu sauki ga duk wata masifa ko Annoba da ta same su, kuma Allah yakan karbi addu’arsu ya kawar masu da duk wata damuwarsu.
“Haka nan kuma zan yi amfani da wannan damar wajen yaba wa Gwamnan jihar mu ta Bauchi Senata Bala Mohammed (Kauran Bauchi), bisa jin kai da karancin da yake nunawa al’ummar jihar Bauchi a kan wannan Annoba ta Cutar Kwaronabairus da ta addabi al’ummar duniya a yau. Kuma ina mai roko ga Allah da ya kara bashi koshin lafiya da ga zazzabin wannan ciwo ya kuma bashi kwarin guiwa da basirar sauke nauyin da aka dora masa na jagoranci a cikin nasara.

“Haka nan Ustaz Suleiman ya yi amfani da wannan dama wajen isar da ta’azziyarsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa rasuwar shugaban ma’aikata na Gwamnatin tarayya marigayi Abba Kyeri, ya kuma yi addu’a wa Allah ya yafe masa ya ba iyalansa da shugaban kasa da daukacin al’ummar kasar nan juriyar rashinsa, Amin,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: