Mohammad Albarno">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Korona Ta Fara Zama Shubuha A Nijeriya

by Mohammad Albarno
August 23, 2020
in MAKALAR YAU
3 min read
Bazuwar Cutar Korona A Nijeriya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Annobar cutar Korona, wanda ta addabi kasashen duniya, tare da ruguza harkokin shige da fice na kasuwanci, ta kuma zama barazana ga rayuwar dan Adam tare da tsaida komai na harkokin rayuwa. Cutar wanda ta samo asali ne tun shekarar 1965, wanda sai a shekara ta 2019 ta bayyana a kasar Sin, wanda akalla a yanzu sama da mutane dubu 84 sun kamu da ita, mutane dubu 4 ne suka mutu, yayin da sama da mutane dubu 79 suka samu nasarar warkewa.

Ta ko’ina, a kowane bangare na kasashen duniya sun yi imanin cewa akwai wannan cutar, musamman ma kasar Amurka da ta ke ganin kanta a matsayin Supa pawa, duk da haka su ma Koronar ta musu wawan kamu, wanda a halin yanzu ko kasar Sin da abin ya fara faruwa akan su ba su kai su yawan mutane masu kamuwa ba. Akalla sama da mutane Miliyan 5 ne suka kamu da cutar, yayin da akalla mutane 164,245 sun mutu, mutane 2,490,711 kuma sun samu nasarar warke wa.

samndaads

Duk da wannan barazanar, kasar Nijeriya da ke Afrika, su ma akwai tabbacin cewa akwai Korona, duba da yadda aka ga Shugaban Fadar Shugaban kasar Nijeriiya, Malam Abba Kyari ya kamu da cutar, wanda har yayi sanadiyyar ajalin sa. Tare kuma da tabbacin cewa Gwamnan jihar Bauch, Alhaji Bala Muhammad ya kamu da ita, da kuma Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Ahmad El-rufa’i, amman abin mamaki shi ne ganin yadda mutane ba su gamsu da cutar ba har yanzu.

A Nijeriya, Annobar cutar ta Korona, an samu tabbacin akalla mutane 46,140 ne suka kamu da cutar, 942 kuma suka mutu yayin da 33,044 kuma suka samu warkewa daga cutar. Wannan lissafin na Gwamnatin tarayyar kasar kenan, wanda hukumar kula da cutar ta NCDC ta bayyana a shafin ta na Intanet, sai dai Al’umma na ganin cewa, wannan cutar batakai ace an hana komai a kasar ba, musamman duba da yadda Kalandar Makaratun Jami’a da na sauran makarantu na lalacewa.

Cutar ta fi tsauri ne musamman a garin Legas, wanda ta fi ko’ina kasuwanci da hada-hada a Nijeriya, abubuwa sai kara tsada suke, al’umma na shiga halin ha’ula’I saboda wannan dokar dakatar da zirga-zirga. Wani daga unguwar Yaba, ya bayyana cewa “abubuwa sunyi tsada sosai, musamman suga kafin cutar ana sayan sa 150, yanzu kuma farashin ya Ninka inda yanzu ana siyar wa 300. Taliyar 200 ta koma 270,  saboda an rufe kamfanoni.”

Wasu kuma saboda rashin hanya mai kyau, motocin safarar kayayyaki sun yi tsada. Duk da sau 3 ake bude kasuwanni a jihar, tare kuma da zirga zirga amman kaya sun karanta a kasuwanni saboda tashin farashin kudin mota.

Wannan dalilin ne yasa, mutane suka gaji da batun Korona, suna ganin takura ne ace sau uku kawai za a rinka harkokin kasuwanci, wasu kuma na ganin dokikin nan da ake cewa ba za a bude makarantu ba kamar ci baya ne, wasu kuma na ganin cutar ba tayi wani tasirin da zai kai ga kulle majarantu, tare da takurawa al’umma ba.

Yayin da wasu na ganin wannan cutar kamar kasuwanci ne gwamnatin kasar ta ke yi, ta fake da cutar saboda siyasar duniya. Domin tana koyi da iyayen ta irin su Amurka da Ingila.

Wasu kam cewa suke, sam babu cutar ma a Nijeriya, domin da akwai da anfi haka kamuwa da cutar, da kuma mutanen da za su mutu sai sun fi dubu 50, kamar yadda yake gani a kasar Amurka.

Wasu sun ce, “idan da abce cutar gaskiya ce a kasar, to tabbas irin yadda ake cunkoso a kasuwannin Idumota na jihar Lagos, da Balugun ta CMS, da kuma sauran kasuwanni irin su Alaba, da kuma yadda ake shiga mota, da yawan adadin mutanen da suke kamuwa da cutar a kullum da yafi haka”.

Wasu kuma na cewa, “ah ah, Allah ne ke kiyayewa, cutar akwai ta, amman Ubangiji na kiyaye bayinsa”. Wasu na ganin shin Saudiya babu bayin Allah ne, kuma shin Madina babu Bayin Allah ne, amman wannan bai hana cutar yaduwa a kasar ba”.

A dai dai lokacin da gwamnatin Nijeriya ta sassauta sabuwar dokar hana zirga zirga, tare da amince wa yara masu rubuta jarabwar kammala sakandare WAEC su koma makaranta, wasu na ganin ya kamata gwamnati ta bude sauran makarantu, idan ma tsaurara dokar za a yi, gwara ayi shi a bakin kofar shiga makarantu, kamar yadda ake yi a bankuna kafin amincewa da bude ko wanne reshe nasu a nahiyar kasar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sharhin Fim Din ‘Kuskure Na Ne’

Next Post

Samar Da Tsaro Ne Babbar Nasarar Gwamnatin PDP A Zamfara -Zannan Gusau

RelatedPosts

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

by Mohammad Albarno
24 hours ago
0

Ni da ma tun da farko ban taba tunani ko...

Rance

Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

by Mohammad Albarno
3 days ago
0

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD), Ya kamata mu sani cewa...

Ilimi

Satar Dalibai Ko  Kassara Ilimi A Arewa?

by Mohammad Albarno
5 days ago
0

alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695: A yanzu babu abinda ya fi jan...

Next Post
Samar Da Tsaro Ne Babbar Nasarar Gwamnatin PDP A Zamfara  -Zannan Gusau

Samar Da Tsaro Ne Babbar Nasarar Gwamnatin PDP A Zamfara -Zannan Gusau

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version