Zubairu M Lawal" />

Korona Ta Kashe Mutum 27 A Nasarawa, Ana Tsimayen Sakamakon Gwajin Mutum Dubu – Gwamna Sule

Gwamnan Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bayyana cewa karuwar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar na da nasaba da yawan gwaje-gwajen da ake yi a fadin jihar a kullum.
Gwamnan ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, Nasarawa ta samu mutum 1,496 da suka kamu da cutar daga cikin mutum 15,023 da aka yi musu gwaji, kuma ana ci gaba da jiran sakamakon na wasu mutum 1000 har yanzu.
Ya kuma kara da cewa, an sallami mutum 743, yayin da wasu 56 ke karbar magani yanzu a Asibitin Dalhatu Araf da ke  Lafiya da Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Keffi. Sannan an samu asarar rayuka 27.
Ya kara da cewa kananan hukumomi uku da suka hada da Lafiya, Keffi da Karu har yanzu suna ke da mafi yawan wadanda suka kamu da cutar, wanda ya kai kashi 80.
Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar da su cigaba da  kula da hanyoyin magance yaduwar cutar  domin rage kalubalen da jihar ke fuskanta.
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana haka a sailin da ya jagoranci zaman taron Majalisar zartarwa ta Jihar.
Gwamna Sule ya kara da  cewa duk da matsalar tsaro da ta addabi jihar, musamman a yankin karamar hukumar Toto, har yanzu Nasarawa na cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a kasar.
Gwamnan ya tabbatar wa mutanen jihar cewa duk da kalubalen tsaro da ke fuskantar jihar a wasu guraren, jihar Nasarawa na ci gaba da samun zaman lafiya.
Sannan ya nuna godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an tsaro, a kan kokarin da suke yi na tabbatar da kawo karshen ‘yan ta’dda da suka hada  ‘yan fashi, ‘yan boko haram a cikin jihar.
Ya ce  dole mu yaba wa shugaban kasa kan daukar matakin gaggawa,  na tura jami’an tsaro don tunkarar ‘yan ta’addan da ke addabar al’umma a  kusa da Tunga da Bakono, mu yi murna da aikin jami’an tsaro da sojojin  da ke ci gaba da fatattakar ‘0yan bindigar.
Gwamnan ya yi amfani da damar taron ya kuma gode wa Ministan Noma da Raya Karkara, Alhaji Sabo Nanono, wanda ya kawo ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar.
Gwamna Sule ya nuna godiya ga Ministan da tawagarsa, bisa kyakkyawan aikin da suka gudanar yayin ziyarar, da kuma ayyukan da suka kawo jihar, musamman tabbatar da cewa an zabe Nasarawa don ta zama jihar da za ta fara aiki na shirin zamanantar da kiwon dabbobi na kasa (NLTP), tare da gwamnatin Netherlands inda ta amince da kashe Yuro dubu 400 don fara aikin.
Gwamnan ya kuma yi godiya ga manyan kamfanonin noma da ke aiki a jihar, da suka hada da Shabu Farms, a karamar hukumar Kokona, rukunin kamfanin Dangote, Olams, da sauransu, saboda goyon bayan da suka ba su yayin ziyarar ta hanyar baje kolin ayyukansu daban-daban.

Exit mobile version