Sulaiman Ibrahim" />

Korona Ta Kashe Tsohon Shugaban Kasar Ghana, Rawlings

Tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings ya rasu sakamakon fama da cutar Korona.

Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya rasu ne a asibitin koyarwa na Korle-Bu da ke Accra, babban birnin Ghana, da safiyar Alhamis.
Rawlings, yayi shugabanci a mulkin soja, ya shiga siyasa ya jagoranci Ghana daga 1981 zuwa 2001.
Ya jagoranci mulkin soja har zuwa 1992, sannan ya yi wa’adi biyu a matsayin zababben shugaban Ghana a dimokaradiyya.

Sannan ya yi murabus daga aikin soja, shi ya kafa jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), kuma shi yafara zama shugaban kasa na farko a Jamhuriya ta Hudu.

An sake zabensa a 1996 domin karin shekaru hudu. Bayan wa’adin mulki biyu a shugabanci, Rawlings ya amince da mataimakinsa John Atta Mills a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2000.

An haife shi a ranar 22 ga Yuni, 1947.

Exit mobile version