Connect with us

MANYAN LABARAI

Korona Ta Koya Ma Na Hankali – Buhari

Published

on

A ranar Talata ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya ta dauki darasi na hankali daga annobar cutar Korona, inda wasu daga cikin kasashen masu arzikin mai sun yi amfani da danyen mai wajen bunkasa tattalin arzinsu da kuma masana’antunsu, amma Nijeriya sabanin hakan a ka samu.

Shugaban Kasa ya bayyana hakan ne a Abuja, Babban Birnin Kasar, lokacin da ya ke kaddamar da aikin bututun gas na Ajakuota-Kaduna-Kano.

“Kasashe masu karfin tattalin arziki sun fuskanci irin wannan mataki na adana iskar gas a Nijeriya, amma sai dai su su na da tsare-tsare, wadanda su ka yi amfani da shi wajen bunkasa tattalin arzikinsu ta hanyar yin amfani da gas. Wannan shi zai bayar da damar jan hankalin masu zuba jari da kuma samar da ayyukan yi ga mutane,” in ji shugaban.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa, gwamnatin Nijeriya tana kokarin wajen kammala aikin saka bututun gas a lokacin da aka kayyade. Ya ce, idan aka samu nasarar kammala wannan aiki zai amfanar da dinbin mutane. Ya bai wa ma’aikatan mai ta kasa (NNPC) tare da takwaranta umurnin mayar da hankali domin kammala wannan aiki, wannan aiki yana daya daga cikin alkawarin da gwamnatin ta yi a zangon mulkinta na biyu da farfado ta tattalin arziki da kuma kara ababan more rayuwa.

Gwamna Jihar Kogi, Yahaya Bello tare da takwaransa na Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai sun yaba da wannan aiki na Ajaokuta da Rigachikun, yayin da shugaban kasa ya ke kallonsu a faifan bidiyo a garin Abuja.

“Mun yi  alkawarin samar da gas a cikin kasar nan domin samun damar gudanar da harkokin kasuwanci a fannin gas,” in ji shugaban kasa Buhari.

Da ya ke bayyana amfanin wannan aiki, shugaban kasa ya bayyana cewa, aikin zai dauki tsawon sharubiyu kafin a kammala. Ya ce, aiki zai samar da wutar lantarki da kuma masana’antu gas wanda wabbab ba karamin ci gaba ba ne. Ya kara da cewa, idan aka samu nasarar kammala wannan aikin, zai bayar samun masana’antun gas a garuruwan Kogi da Abuja da Neja da Kaduna da kuma Kano.

Shugaban kasa ya ci gaba da cewa, cutar Korona ta zaburar da wannan gwamnati wajen muya gurbin hanyoyin tattalin arziki da kuma bunkasa kayayyakin cikin gida Nijeriya. Shugaban kasa ya bukaci kamfanoni  masu zaman kansu su yi amfani da wannan dama na inganta kasa da albarkatun gas.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: