Korona Ta Sake Kashe 10, Ta Kama 397 A Nijeriya Shekaranjiya

Korona

Daga Khalid Idris Doya,

A ranar Litinin an samu rahoton cewa mutum 397 ne suka kamu da cutar Korona a jihohi sha takwas na Nijeriya.
A bayanan kullum-kullum da hukumar dakile yaduwar cutuka (NCDC) ta ke wallafa a shafinta, ta ce a ranar 28 ga watan Disamban ta samu sabbin wadanda suka kamu da cutar Korona mutum 397 da kuma mutum 10 da suka mutu sakamakon cutar.
Rahoton hukumar na cewa zuwa yanzu mutum 84811 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar, inda aka sallami mutum 71357 da suka warke daga cutar.
Zuwa yanzu cutar ta kashe mutum 1264 a jihohi 36 na Nijeriya ciki har da babban birnin tarayya Abuja tun lokacin da cutar ta barke a Nijeriya.
Sabbin kesa-kesan da aka samu na mutum 397 daga jihohi 18 sun hada da jihar Legas mai mafi yawan mutane (144) sai jihar Fitato wanda aka samu mutum (83), Kaduna (48), Adamawa (36), Ribas (22), Oyo (16), Kebbi (10), Nasarawa (7), Sokoto (7), FCT (5).
Sauran jihohin sun kunshi, Kano mai mutum (5) da suka kamu Edo (4), Jigawa (3), Ogun (2) Akwa Ibom (2), Neja, Bauchi da jihar Zamfara masu mutum daya-daya.

Exit mobile version