Connect with us

KASASHEN WAJE

Korona Ta Sake Kashe Amurkawa Sama Da Dubu 2 A Rana Guda Tak

Published

on

 

Jami’ar Johns Hopkins da ke sanya ido kan yadda cutar Korona ke yaduwa a Amurka ta ce a shekaran jiya mutane sama da dubu 2 suka mutu sakamakon wannan annobar ta Korona.

Alkaluman da Jami’ar ta bayar sun nuna cewar mutane dubu 2 da 53 suka mutu a shekaran jiya sabanin 2,502 da aka samu a ranar Laraba, abinda ya kawo adadin wadanda cutar ta kashe a Amurka zuwa 62,906.

Kwanaki 3 da suka gabata ne dai jami’ar ta Johns Hopkins da ke Amurka tace annobar ta Korona ta hallaka mutane dubu 2 da 502 a fadin kasar a cikin sa’o’i 24 a tsakanin ranakun Talata da kuma Larabar da suka gabata, wato 28 da kuma 29 ga watan Afrilu.

Annobar Korona dai na ci-gaba da yiwa Amurka ta’adi fiye da kowace kasa a duniya, inda a yanzu haka ta hallaka jimillar mutane dubu 61 da 717.

Advertisement

labarai