Mustapha Ibrahim" />

Korona: Wajibi Ne Al’umma SU Bi Umarnin Shugabanni – Faggacin Gaya

Mai Girma Alhaji Faruku Umar danlassan, Hakimin Warawa kuma Fagacin Masarautar Gaya, ya bayana cewa wajibi ne al’umma ta yi biyayya da dukkanin umarnin shugabanni da bai saba wa shari’a ba kuma wajibi ne al’umma ta bi umarnin shugabanni na yaki da cutar Korona da ta zama alkakai a duniya kuma shugabanni sun yi umarni ne domin kare al’ummarsu daga dukkan abunda ka iya cutar da su dan haka wajibi ne abu umarnin shugabani a tab akin Faggacin Gaya Hakimun warawa da ke jahar Kano a Najeriya.

Hakimun wanda ya wakilci mai martaba sarkin Gaya, Dr Ibrahim Abdulkadir, ya bayana haka ne a wajan bikin bude masalacinj Jumaa a kauyen Yar Dalla da dan majalisar jaha kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki ta Jahar kano Hon Abdul Madari ya gina a kauyan Yar Dalla, haka kuma hakimun ya ce wajibi ne musulmi su koma ga Allah ta hanyar bin dokikin Allah sau da kafa ta hanyar bin umarnisa da barin abunda ya hana yin haka da addua shi ne baban maganin ko wace masifa.
Shi ma sabon limamun masalicin Jumaa na Yardalla Imam Malam Garba sulaiman Yardalla, ya bayana a cikin hudibarsa ta farko masalacin jmaar cewa akwai bukatae alumar musulmi su hada kansu wuri guda kuma a guji munafunci domin munafunci mumunar dabia ce da ake a zabtar da munafiki fiye da kafuri dan haka aguji muna funci mumunar dabia ce ta halaka
A karshe Hon Hassan Jibrin Yardalla wanda akafi sani da mai Rago da Hon Adananu Musa danlasan yabawa sukayi ga dan Majalisarsu Hon Madari da sauran shugabani da suka bada gudimawa kan gina masalacin Juma
a da ya yi a Garin Yardalla.

Exit mobile version