Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa watakila a dakatar da wasannin firimiyar Ingila idan har aka ci gaba da samun ‘yan wasa ko jami’ai masu dauke da cutar a kungiyoyi daban-daban.
A satin da ya gabata ne Fira ministan Birtaniya Boris Johnson ya saka dokar kulle a fadin kasar sai dai ya ce sababbin matakan sake killace al’ummar kasar da gwamnatinsa tayi ba zasu shafi wasannin kwallon kafa na Firimiya da sauran nau’ikan fitattun wasannin kwararru a Ingila ba.
Boris Johnson ya yin jawabi ta kafar talabijin ya sake sanya dokar kulle da zai shafi Kusan mutane miliyan 56 a Ingila, mai yiwa har zuwa tsakiyar watan Fabrairu, domin magance kaifin yaduwar cutar korona da ta sake bulla a karo na biyu.
Matakan, wadanda suka hada da rufe makarantun firamare da sakandare, za su fara aiki ranar Laraba, bayan da kasar Scotland ta sanar da makamanciyar da ta fara aiki tun daren jiya domin kare mutanen kasar daga cutar Korona.
Da farko anyi zaton za’a sake tsayar da harkokin kwallon kafa a kasar gaba daya sakamakon yadda cutar ta dawo da zafinta sai dai hakan bai kasance ba inda kuma aka bayar da damar ci gaba da buga wasa tare da bin dokokin cutar da gwamnatin ta birtanya ta gindaya.
A ‘yan kwanakin nan an samu ‘yan wasa da dama a gasar ta firimiya da suka kamu da cutar wanda hakan yasa aka dakatar da buga wasu daga cikin wasannin firimiya a satin daya gabata ciki har da wasan Manchester City wanda aka tsayar.
Sannan ana ci gaba da samun karin masu kamuwa da cutar a kullum dalilin da yasa wasu daga cikin masu fada aji a harkar kwallon kafar Ingila suka bayyana cewa akwai bukatar a sake dakatar da gasar ta tsawon wata daya.
Tuni dai daman aka dakatar da wasu wasanni ba’a buga ba saboda kamuwa da cutar da wasu ‘yan wasa sukayi sannan cutar ce tasa ‘yan wasan Aston Villa basu fafata a wasan da Liverpool ta doke su ba a gasar FA ta ranar Juma’a.