Connect with us

LABARAI

Korona: ’Yan Nijeriya Mazauna Waje 40 Suka Rasu – Abike Dabiri

Published

on

Kimanin ’yan Nijeriya mazauna kasashen waje 40 ne su ka rasu sakamakon kamuwa da cutar Korona.

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Nijeriya Mazauna ketare, Mrs Abike Dabiri-Erewa, ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a a wani shirin gidan kafar talabijin, wanda a ka gudanar a yayin da ta ke bayyana irin kokarin da Gwamnatin Nijeriya ke yi wajen kula da jin dadi da walwalar ’yan Nijeriya da ke wajen.
Ta kara da cewa, gwamnatin kasar ta na tuntubar ’yan Nijeriya da ke sassan duniya daban-daban kuma a na nan a na kokarin ganin an dawo da su gida.
Bugu da kari, shugabar ta bayyana cewa, “’Yan Nijeriya mazauna waje su na yin wani hannu waje guda, don hada gidauniyar taimaka wa ma’aikatan lafiya da ke cikin kasar, kuma ba da jimawa ba za a gabatar da yunkurin ga kwamitin musamman na fadar shugaban kasa kan annobar Korona.”
Game da batun dawowar ’yan Nijeriya da su ka makale a kasashen duniya bayan barkewar annobar cutar ta Korona, shugabar hukumar ta ce, wasu ’yan kasar 18 ne za su iso Nijeriya a cikin karshen makon da ya gabata daga kasar Faransa.
“Za su dawo gida ne ba tare da biyan ko Sisin Kwabo ba. Godiya ga ambasadonmu da ke Faransa,” in ji ta, wacce ta kara da cewa, abinda ya ke damun ta shi ne, yadda har yanzu akwai wasu tsirarun ’yan Nijeriya da ke zaune a gidan yari a kasar Indonesiya sakamakon ta’ammali da kwayoyi, inda ta kara da cewa, a na kokarin yin yarjejeniya tsakanin kasar da Nijeriya, don ganin an saukaka hukuncin da za a aiwatar mu su.
“Hukumcin kisa ne kan duk wanda a ka kama da laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi a Indonesiya. To, wannan matsalar ce mu ke kokarin warware ta… mu na rokon su da kada su kashe su, amma su na cewa, ai haka dokarsu ta ke.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: