Connect with us

JAKAR MAGORI

Korona: ‘Yan Sanda Sun Damke Mutum 18 Su Na Liyafa Tsirara

Published

on

Wadanda ake tuhumar an kama su ne ranar Lahadi a Nairobi suna gudanar da liyafar tsirara, yayin da ake aiwatar da dokar hana zirga-zirga a sharadin kwanaki 14 da hukuma ta sanya, za a gurfanar da su a kotu domin fuskantar tuhuma.

Sakataren riko na cikin gida Karanja Kibicho ya ce wadanda ke tsare za a yi maganin su.

An kuma kama mutane a shingen tituna, sanduna, majami’u, bukukuwan aure da sauran ayyukan sirri.

“Wadannan mutane ne da ke ci gaba da barazana ga rayuwar wasu kuma idan muka dauki mataki sai su koka,” in ji shi.

Shekarun wadanda aka cafke din tsakanin 14 zuwa 30, an tsare su ofisoshin ‘Yan Sanda na Kilimani. Shugaban ‘Yan Sanda na yankin Lucas Ogara ya ce waDanda ake zargin, ciki har da mata biyar, za a gurfanar dasu gaban kotu kuma suna fuskantar tuhume-tuhume iri daban-daban karkashin dokokin kiwon lafiyar jama’a.

Bisa ga abin da muka samu a bidiyo mun gan su a wani gida mai daki guda suna gudanar da sha’aninsu.

Ko ma yaya, mafi yawan labarin da ake yadda wa a titinan da aka gina a biranen Nairobi, Mandera, Kilifi, Mombasa da Kwale ba gaskiya bane.

“Mun ga lokuta da yawa masu ban dariya a wadannan hanyoyin, wasu mutane sanye da bandeji, wasu kuma karya suke yi don kawai a ba su izinin ketare shinge. Ba za a hana wadanda ke neman magani, da ke bukatar tiyata ko kuma yin aikin likita na gaggawa don ganawa da su ba, ”in ji Kibicho.

Ka tuna cewa a Nijeriya, kwanan nan ‘Yan Sanda sun kama mutane 39 a wani katafaren kulob din Legas.

Dangane da bayanin da Bala Elkana, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ya fitar, ya ce,‘ yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Idimu sun kama mutane 39 a wani filin wasa a Idimu da misalin karfe 1:30 na safiyar Juma’a, 24 ga Afrilu.

Elkana ya kuma bayyana cewa, an kama mutane 10 ranar alhamis saboda shirya wani biki a Lekki Garden, in ji jami’in ‘Yan Sanda na Kenya ya ba da misali.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: