Korona: Zakakuran ‘Yan Wasan Tunisia Ba Za Su Buga Wasa Da Nijeriya Ba

Daga Sulaiman Ibrahim,

Wannan zai zama babban koma-baya ga Carthage Eagles ta Tunisia, manyan ‘yan wasa da kociyan kungiyar, Mondher Kebaier, ba za su sami halartar karawa da Super Eagles a filin wasa na Roumdje Adjia, Garoua, Kamaru, ayau Lahadi.

A wata hira da aka yi a ranar Asabar, mataimakin kocin Tunisia, Jalal Al-Qadri, ya ce akalla ‘yan wasa 12 a Tunisia suka kamu da Korona kuma ba za su buga wasan da Nijeriya ba.

’Yan wasan su ne Wahbi Khazri, kyaftin din da ya zira kwallaye biyu a wasan da suka doke Mauritania 4-0, Aissa Laidouni, Dylan Bronn, Ghaylène Chaalali, Ellyes Skhiri, Anis Ben Slimane, Mohamed Romdhane, Ali Maâloul, Ben Hmida, Aymen Dahmen Yoann Touzgha da kuma Issam Jebali.

Exit mobile version