Connect with us

MAHANGA

Koronabairos: Annobar Da Ta Mamaye Duniya

Published

on

Wannan cuta ta Koronabairos za mu iya cewa wacce a ake yayi, ta fara kamar wasa, ana ganin a kasashen Turawa ne kawai ta ke, ana haka sai ga shi ta shigo Afrika har ta shigo Nijeriya. Lokacin da ta shigo kasar nan, jama’a da dama, musamman talakawa sun dauka cutar manyan mutane ce, bisa la’akari da cewa manyan ne suka fara kamuwa da ita.
To, amma da tafiya ta yi tafiya sai ya zama ruwan dare mai gama duniya. Ko a lokacin da ta shigo, ta fara ne da Abuja da Legos, inda a nan ne ake da manyan filayen jiragen sama masu samun yawan jiragen da ke shigowa daga kasashen waje. Don haka sai waau suka dauka cewa ai kila sai wanda ya je kasar wajen ne zai iya kamuwa ita.
Ganin haka sai Hukumomi da masana a harkar kiwon lafiya suka dukufa wajen wayar da kan jama’a, inda ake nuna cewa abin ba a nan ya ke ba, cuta ce da za ta iya kama kowane irin mutum, don haka babbar hanyar kauce wa kamuwa da ita, ita ce ta hanyar daukar matakan da suka dace.
Haka kuma Hukumomi da sauran masana a kan harkar kiwon lafiya sun bayar da shawarwarin yadda za a magance yaduwar wanan cuta, inda Hukumomin suka sanya dokokin da suke ganin idan aka bi su za a iya rage yaduwarta a cikin jama’a. Su kuma masana harkar kiwon lafiya suka shiga bayar da hanyoyin bi don kauce wa kamuwa da cutar.
Hukumar a gwamnatin tarayya da jihohi sun sanya dokoki, inda Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a jihohin Legos da Ogun da kuma Abuja har na tsawon mako biyu, wanda bayan kammala makwanni biyun sai aka ga abin kara lalacewa yake yi, don haka sai shugaban ya kasa wasu makwanni biyu, wanda kuma shi ne muke ciki.
Haka su ma jihohi sun sanya irin wannan doka a jhohinsu, kodayake ba duka ba ne suka sanya, amma jihar Kaduna na a sahun gaba wajen sanya dokar, inda aka sanya don rage cunkoson jama’a, wanda ya hada har da wuraren ibada, kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama’a.
Duk da wasu na ganin wannan doka ta yi tsanani, amma su Hukumomi sun kare kansa da cewa babu abin da ya kamata a yi in ba haka ba, domin idan aka bar abin ya yadu, to ba a san irin asarar rayukan da za a yi ba.
Jihar Kano ta kasance cikin wacce ba ta dauki irin wannan doka da wuri ba, amma daga bisani da abin ya fara yaduwa a jihar, sai ya zama ta fi daukar dokar da tsanani, musamman ganin yadda cutar ke yaduwa a jihar tamkar wutar daji.
Daga farkon shigowar wannan cuta a kasar nan, manya suka fara kamuwa da ita. Misali, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-rufai na daya daga cikin wadanda suka kamu da ita, wanda kuma har yanzu yana nan yana jinya. Sannan Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, shi ma ya kamu da ita, amma daga bisani Allah ya warkar da shi, har ya koma cikin jama’a ya ci gaba da aikinsa.
Haka cikin na gaba-gaba a mayan da suka kamu da wannan cuta, shi ne wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Juma’ar nan, wato shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyari, wanda tun bayan dawowarsa daga kasar Jamus aka gwada aka samu yana da ita, kuma tun lokacin bai yi lafiya ba har ya rasu.
To, amma daga bisani ai abin ya zama cewa cutar ta zama kowa na iya dauka, domn jama’a daga matakai daban-daban duk suna kamuwa da ita, wanda hakan ta sa sauran jihohin da ba su sanya dokar hana fitar ba, su ma suka sanya.
Ko shakka babu za mu iya cewa wannan cuta ta zama annoba, wacce ta fara kamar wasa, inda har wasu ma na kallonta abin wasa, wasu ma na cewa karya ce kawai. Amma bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa, yanzu kowa ya shiga taitayinsa.
A nan ne na ke ganin yana da muhimmanci mu rinka ba gwamnatoci hadin kai wajen bin umurnin dokokin da suka sanya don rage yaduwar wannan cuta. Haka kuma mu kasance masu bin shawarwarin Likitoci wajen bin hanyoyin kauce ma kamuwa da wannan cutar.
Cikin hanyoyin da masana kiwon lafiya suka zayyana da cewa idan aka bi su za a samu saukin yaduwar wannan cuta, akwai kauce wa shiga cikin cunkosan jama’a, wanke hannu akai-akai, kiyaye yawan taba hanci, baki da idanu, inda ba wai mutum ya tabatar da cewa hannunsa na da tsafta ba ne.
Haka kuma akwai kiyaye yawan yin hannu da jama’a barkatai. Domin masanan sun yi nuni da cewa idan mutum ya tabbatar yana da tsafta a hannunsa, to bai san wadanda zai je ya rinka yin hannu da su ba, don haka abu mafi a’ala shi ne a kiyaye yawan yin hannu da mutane.
Irin wadannan dokoki akwai wuraren da dole sai gwamnati ta shigo ciki, wanda hakan ta sa gwamnatocin suka sanya dokar hana fita don kada a samu cunkoson jama’a, wanda ya hada har da wuraren ibada, kasuwanni da sauransu. A wasu jihohin ma, da Abuja har kama irin masu karya dokar ake ana hukunta su, musamman masu wuraren ibada.
A nan ne na ke ganin yana da muhimmanci mu bi irin wadannan shawarwari na gwamnatoci da masana harkar kiwon lafiya. Duk dayake wata dokar mutum zai ga tamkar an takura masa n e, amma ina da imanin cewa Hukumomin ba su yi haka ba ne don su kuntata wa jama’a, sun yi ne don taimakon jama’a, ko da kuwa jama’ar ba za su kalli abin a haka ba.
Haka kuma muna rokon Allah mai Girma da daukaka ya kawo mana karshen wannan cuta, ya kare mu daga kamuwa da ita, alfarmar Manzon Sa Muhammad Mai tsira da aminci. Su kuma wadanda suka kamu da ita, Allah ya ba su lafiya.

Advertisement

labarai