Koronabairus: Habasha Za Ta Saki Fursunoni 4, 000 Saboda Rage Cunkoson Gidajen Yari

Kasar Habasha ta bayyana cewa za ta saki dubban fursunoni daga gidajen yarin kasar domin ganin ta rage cunkoson gidaje yarin a wani matakin da kasar ke dauka na dakile yaduwar cutar Koronabairus a kasar.
Ministan shari’a na kasar, Adanech Abebe, shi ne ya tabbatarwa da kafar watsa labaran kasar, inda ya ce matakin na su zai sanya su saki fursuna dubu hudu. Ya kuma tabbatar da cewa wadanda za a saki din sune wadanda aka garkame  sakamakon kananan laifuka da suka aikata da kuma wadanda dama wa’adin fitarsu gidan yarin ya kusa.
Rahoton sashen lura da kare hakkin bil’adama ta Amurka da ta fitar kan kasar Habasha din ta zargi gidajen yarin kasar da cunkoson jama’a kuma wuri da ya kasance  barazana ne ga rayuwar al’umma sakamakon yanayinsa. Sannan kuma akwai karancin ingantaccen ruwan sha, abinci da kuma magunguna.
Kafar watsa labarai ta Africa News ta tabbatar da cewa; har ya zuwa yammacin ranar Talata, mutum 12 kawai aka samu da cutar COVID-19 bayan an gwada mutum 480.
Exit mobile version