Koronabairus: Lauyoyi Sun Jinjinawa Alkalin Alkalai Kan Rufe Kotuna

Lauyoyi sun jinjinawa Alkalin Alkalan Nijeriya, CJN Justice Tanko Mohammad bisa umurnin da ya bayar domin dakatar da dukkanin wani zama a kotuna sai dai idan abin da yake da bukatar zaman gaggawa. Hakan ya biyo bayan bullar cutar COVID-19 a Nijeriya. Inda Alkalin Alkalan ya bayar da umurnin har na tsawon mako biyu.

Lauyoyin sun ce wannnan umurnin abin a jinjina ne domin a cewarsu wanda kawai yake raye ne zai iya yin shari’a tare da neman adalci.

Mrs Florence Dagema, wanda yake ma’aikaciyar shari’a ce a Abuja, ta ce tuntuni ma ta so a ce wannan umurnin ya zo. Amma ta ce gwara a ce an yi latti da ya zama ba a yi ba kwata-kwata. Ta ce kotu wuri ne da yake tara jama’a, kuma akwai wadanda suke zuwa kotun bayan sun dawo daga kasashen waje.

 

Exit mobile version