Connect with us

KASASHEN WAJE

Kotu A Brazil Ta Soke Takarar Lula Da Silba

Published

on

Jam’iyyar tsohon shugaban Brazil Lula Da Silba ta bayyana furucin ta ‘yan lokuta bayan da Alkalan kotu zabe suka yi watsi da bukatar tsohon shugaban kasar na tsayawa takara.
A zaman da Alkalan suka yi a jiya Asabar sun bayyana takarar tsohon Shugaban kasar a zaben ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin abin da ya kaucewa doka.
A watan Afrilu shekarar 2018 bayan share kwanaki uku a cibiyar kungiyar kwadagon ma’aikatan karafe na Sao Bernado, tsohon Shugaban kasar Brazil Lula Da Silba ya mika kan sa zuwa jami’an tsaron Curtiba dake kudancin kasar inda suka tisa keyar sa zuwa gidan kaso da zai share shekaru 12 a tsare bisa laifi rashawa da cin hanci.
A shekarar da ta shude ne wata kotu a kasar ta Brazil ta yanke masa hukuncin dauri bisa laifin karbar rashawa.
Advertisement

labarai