Sulaiman Ibrahim" />

Kotu A Kano Ta Tsare Uwar Gida Kan Kisan ‘Yar Aikinta

Rikicin da ya biyo bayan mutuwar wata ‘yar aikin gida ‘yar shekaru 16 makonnin da suka gabata a Kano ta kai matuka a ranar Litinin bayan gurfanar da uwar gidan a gaban kotun majistare da ke jihar.

Kotun Majistare Mai lamba 8 da ke zaune a yankin Gyadi-Gyadi da ke cikin garin ta ba da umarnin a tsare Fatima Hamza, matar da ake zargi da kashe ‘yar aikinta a cibiyar gyara.

An zargi Fatima Hamza da lakadawa marigayiyar mai aikin gidanta duka bayan zargin cewa wai marigayiyar ba ta yi ayyukan gida da aka umurce ta ta yi ba.

Lauyan gwamnati, Barista Asma’u Ado, ta fada wa kotun cewa an gurfarnar da matar a gaban kotu ne kan tuhuma daya da ake yi mata na aikata kisan kai, wanda ya saba wa sashi na 224 na Dokar Penal Code.

Sai dai cewa, wacce ake zargi da kisan ta musanta aikata laifin.

Lauyanta, Barista Ibrahim Abdullahi Chedi ya nemi belinta a kan rashin lafiyarta, don ta samu barin juna biyunta yayin da take tsare a hannun ‘yan sanda kuma ‘yar jaririyarta ma ba ta da lafiya, inji lauyanta.

Exit mobile version