Balarabe Abdullahi" />

Kotu Ta Ba Da Belin Tsofaffin Ma’aikata Ma Su Addu’a

A ranar Alhamis ce, babbar kotu mai daraja ta daya da ke Dogarawa da Mai shari’a Munnir Ladan ke yi shugabanci, ta amince da bayar da belin wasu korarrun ma’aikata su takwas da gwamnatin jihar Kaduna ta kora daga ayyukan da suke, a dalilin rungumar addu’o’i da suke yi domin su sami hakkokinsu daga gwamnatin jihar Kaduna.
Su dai wadannan tsofaffin ma’aikata da aka bayar da belinsu, tun farko sun bi duk hanyoyin da suka dace domin gwamnatin jihar Kaduna ta biya su hakkokinsu na korarsu da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, amma hakarsu bai kai samun ruwa ba.
A dalilin haka sai tsofaffin ma’aikatan suka hadu, inda suka yi kungiya, da har suka yi ma ta rijista, suka kira ta da sunan kungiyar korarrun ma’aikata da gwamnatin jihar Kaduna ta kora daga ayyukan da suke yisai suka fara yin addu’o’i a wasu ranaku da suka zaba a duk mako, a filin sallar Idi da ke Kofar Doka a Zariya.
B ayan korarrun ma’aikatan sun kammala addu’o’in da suke yi a inda suka saba, sai rundunar ‘yan sanda ta shiyyar Zariya bisa umurnin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna aka damke wadanda ke jagorantar addu’o’in, inda aka gufanar da su a wata kotun majastare da Rigasa a Kaduna.
Wannan kotu, bayan ta saurari karar da ake yi wa wadannan korarrun ma’aikata, sai ta tura su gidan yari, da nufin lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna da suka gabatar da karar su bayar da dalilan da suka sa
suka gabatar da wadanda ake zargi,a gab da ci gaba da shari’ar sai lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna suka janye wannan kara da suka kai korarrun ma’aikatan, suka shigar da sabuwar kara a babbar kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa, inda wani lauya da ke wakiltar gwamnatin jihar Kaduna a wannan karar, Barista Suleman Kufena, ya ce, sun shigar da wannan kara ne, inda suke tuhumar mutum takwas, da suka jagoranci wannan addu’a, da lauyan ya ce, sun yi taron babu izinin hukuma, kuma addu’o’in suna iya gwamnati aikin da ta ke yi. Bayan mai Shari’a Munnir Ladan ya saurari mai kara, sai lauyan wadanda ake tuhuma, Barista Jafaru Abbas Ibrahim, ya bayyana wa kotu cewar,
wadanda aka gabatar da yake karewa, tuni kotun majastare ta Rigasa ta wanke su, babu wani dalilin sake gabatar da su a wannan kotu.
A nan sai Mai Shari’a Munnir Ladan ya ce babu wata takarda da ke nuna an wanke wadanda aka gabatar a gabansa, sai ya nemi jin ta bakin lauyan gwamnatin jihar Kaduna sai ya tabbatar cewar, sabuwar kara suka shigar, kuma a wanke su a wancan kotun ba, a cewar lauyan gwamnatin jihar Kaduna.
Bayan wadanda aka gabatar sun ce su ba su aikata wannan laifi ba, sai nan take Mai shari’a Munnir Ladan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa Alhamis da ta gabata, inda bayan mai gabatar da wadanda ake tuhuma a kotu ya gabatar da wadanda ake tuhuma, sai nan take Lauyan wadanda ake tuhuma, Barista Jafaru Abbas Ibrahim, ya nemi kotu ta bayar da belin wadanda ake tuhuma, nan take lauyan gwamnati ya amince da bukatar lauyan wadanda ake tuhuma, ba tare da bata lokaci ba, Mai shari’a Munnir Ladan ya bayar da belin wadanda ake tuhuma bisa sharadin duk wanda zai tsaya wa ko wane daya zai biya naira dubu dari, aka kuma dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 21 ga watan Maris na wannan shekara ta 2019.

Exit mobile version