Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Ba Jami’ar ABU Wa’adin Bayyana Kudin Tsoffin Ma’aikata Sama Da Bilyan Biyu  

Published

on

Kotun ma’aikata da ke birnin tarayyar Abuja ta baiwa mahukuntan jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kwana bakwai su bayyana ma ta dalilin da ya sa aka cire kudi har naira bilyan 2.5 na ma’aikatan da aka sallama aiki daga makarantar.

Alkaliyar Kotun Mai shari’a Rakiya Haastrup ta yi watsi da jayayyar da babban bankin kasa ya yi tare da kalubalantar takardar da tsaffin ma’aikatan suka gabatar, na neman kudin daga asusun ajiyar bankin makarantar.

CBN ya nemi kotun da ta yi watsi da takardar da tsaffin ma’aikatan suka gabatar a gaban kotun ne kan cewa ba su da sahihanci.

Lauya mai tsayawa Bankin Ekokoiesua Urua, ya nemi yin watsi da takardar a bisa hujjar cewar sai an nemi izinin akanta janar na kasa tukuna kafin a taba asusun bankin.

Lamarin ya biyo bayan korar ma’aikatan jami’ar ne su 110 a shekarar 1996 a lokacin da Manjo Janar Mamman Kotangora  ya yi rikon kwarya na shugabancin jami’ar.

Ma’aikatan sun taso da ikirarin ne a a shekarar 2012 ta hannun lauyan su Femi Falana  bayan da mahukuntan jami’ar suka gaza wajen aiwatar da matakin takardar binciken kwamitin da aka kafa a shekarar 1999 da shekarar 2004 da kuma ta shekarar 2011, wadda suka bayar da umarnin a mayar da ma’aikatan kan aikinsu da kuma biyan su hakokin su.

Alkali P.O. Lifu na kotun a wancan lokacin a  cikin watan Nuwambar shekarar 2015, ya yanke hukunci a kan cewar, ba a bi ka’ida wajen sallamar ma’aikatan ba, inda ya kuma bayar da umarnin da a biya ma’aikatan hakkokin su na naira biliyan 2.5.

Maishari’a Rakiya Haastrup ta dage sauraron karar zuwa ranar ashirin da hudu ga watan Yuni don ci gaba da sauraron karar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: