Daga Bello Hamza,
A ranar Talata data gabata ne wata kotun yanki da ke Gwagwalada, Abuja ta bayar da belin wani magidanci mai suna Bamidele Lamidi, akan kudi Naira 250,000 akan zargin da ake yi masa na zamba cikin aminci.
Lamidi wanda mazaunin garin Gwagwalada ne, ya musanta aikata laifin a yayin da aka karanto masa.
Da yake yanke hukuncin, alkali Sani Umar ya umarci wanda ake zargin ya samar da mutum daya da zai tsaya masa.
Daga nan ya kuma umarci a wuce da shi gidan yarin Suleja in har ya kasa cika wadanda sharuddan.
Ya kuma daga karar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu don cigaba da sauraron shari’ar.
An dai gurfanar da shi ne bisa tsayawa wani mai suna Abubakar Nmadu da ya yi wanda ya karbi bashin Naira miliyan 1 a bankin Grant Microfinance Bank.
Salihu tare da abokin harkar sa sun kuma kasa biyan kudin.
Ya ce, laifin ya saba wa shashi na 312 da 322 na dokar Fanel Kot.