Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Kotu Ta Bada Umarnin  A Kama Jay-Jay Okocha Saboda Kin Halartar Zaman Kotu

Babbar kotun jihar Legas ta bada umarnin kama tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafan Nijeriya, Austin Jay Jay Okocha sakamakon rashin halartar zaman kotun da bai yi don amsa wasu tambayoyin zargin da ake mi shi na rashin biya kudaden haraji.

An  rawaito cewa mai kara, Dakta Jide Martins, ya shigar da kara ranar 6 ga watan Yunin shekarar  2017, amma wanda ake karar ya ki ya bayyana a gaban kotu don ya kare kanshi bisa tuhumar da ake mishi.

Mai karar ya bayyana wa kotu cewa wanda yake karar yi ki zuwa ofishin hukumar haraji dan biyan harajin da ya kamata ya biya, mai shari’a all Adedayo Akintoye, a ranar 29 ga watan Janairu ya bada umarnin kama shahararran dan wasan kwallon kafan bayan dage sauraron shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu.

Saidai, mai karar bai sa an kama wanda yake karar ba har zuwa waadin da alkalin ya bayar. Har ila yau, alkalin ya sake bada umarni kama wanda ake zargin zuwa ranar da zai sake sauraron karar. Anyi kokarin jin ta bakin Okocha akan lamarin saidai abin yaci tira sakamakon rashin daga waya da shi Okochan yayi.

Okocha dai shahararran dan wasan farko da aka gurfanar a  kotun Nijeriya a bisa zargin kin bayin kudin haraji, shahararrun ‘yan wasa na duniya irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun fuskanci irin wannan tuhumar a kasar Spaniya,wannan ya nuna cewa indai akayi nasara a wannan karar da akayi a kan Okocha, yawancin ‘tan wasan Nijeriya wanda suka dowa gida bayan sun kammala buga kwallo kafa a nahiyar Turai zasu fuskanci irin wannan tuhumar a jihohin su.

Exit mobile version