Daga Sagir Abubukar,
Alkalin Kotu Shari’ar Musulunci da ke Katsina, wato (Upper Shari’a ii) mai shari’a Sagir Imam ya bada umurnin kamo dan gwagwarmayar nan, Alhaji Mahadi Shehu, dan asalin jihar Katsina azaunin garin Kaduna, bisa karar da sakataren gwamnati jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya shigar a gabanta, akan zargin bata masa suna.
Mai shari’a ya bada umurnin biyo bayan wani hukunci da ya yanke a ranar (16/12/2020) kan yadda aka isar da sakon sammace da aka hannan ta mashi a Abuja, inda lauyan sa ya ce ba abi hanyar da ta dace ba.
Da ya ke yanke matsayar kotun, Mai Shari’a Sagir Imam, duk da lauya wanda ake zargin Barista Abbas Abdullahi Macika, ya san yau ne ake zaman ci gaba da sauraren shari’a, bayan kotu ta yi watsi da rokan Wanda ake Kara a ranar 16/12/2020, inda ta bada damar wanda ake kara Mahadi Shehu da ya halarci kotu a yau laraba, ga shi bai zo ba, lauyan sa bai zo ba, kuma babu wata takardar sanarwa da aka kawo gaban wannan kotu. Wannan ya nuna ya raina wannan kotu, don haka kotu ta yi umurnin cewa a kamo Mahadi Shehu, a gabatar da shi gabanta, domin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi a karkashin sashe na (300) na (Shari’a penal code.)
Alkalin Sagir Imam ya dage ci gaba da sauraren shari’a zuwa ranar 13/01/2021, domin ci gaba da sauraren karar.