Kotu Ta Bada Umurnin A Gaggauta Sakin Tsohon Sarkin Kano Sanusi II

Kotu ta umarci a baiwa Sarki Muhammadu Sanusi II damar shiga ko ina a Nijeriya ban da Kano.

Haka kuma kotun ta ba da kwana uku a mika wannan hukuncin da aka yanke ga wadanda aka kai karar kuma su yi aiki da ita.

Wadanda aka kai karar sun hada da hukumar tsaro ta farin kaya, da Sufeto-janar na ‘yan sandan Nijeriya, da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da kwamishinan shari’a na jihar Kano da kuma ministan shari’a na Nijeriya.

An dage zaman kotun sai ranar 26 ga wannan watan na Maris din nan da muke ciki.

Exit mobile version