Babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta amince da karar da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS suka shigar gabanta suna neman su ci gaba da garkame tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore har na tsawon kwana arba’in da biyar domin gudanar da bincike a kansa. Sowore wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters an kama shi ne a ranar Asabar bisa shirya zanga-zangar juyin juya hali da suka yiwa take da #RevolutionNow.
Hukumar DSS din na zarginsa da kokarin tada zaune tsaye bisa shirya wannan zanga-zangar. Jami’an tsaron na DSS ne suka nemi kotun ta ba su damar ci gaba da garkame Sowore ne har na tsawon kwana 90, inda Alkalin DSS din, G.O Agbadua, ya ce DSS din na da bukatar wadannan kwanaki domin bincikarsa.
Sai dai a shari’ar da aka gudanar a ranar Alhamis, mai Shari’a Taiwo Taiwo ya amince da a ci gaba da rike shi ne kawai na tsawon kwana 45 domin kammala bincike akansa.
Kwanakin na shi, zai fara ne daga 8 ga watan Agusta.