Bello Hamza" />

Kotu Ta Ce A Kwace Gidajen Patience Jonathan Na Abuja

Babban kotun tarayya dake Abuja ta zartar da hukuncin wucin gadi na kwace gidaje biyu na Misis Patience Jonathan matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathana shari’a da aka gudanar ranar Litinin.

Gidajen na Plot No. 1960, Cadastral Zone A05 a unguwan Maitama daya kuma na Plot No. 1350, Cadastral Zone A00 dukkansu a babban birnin tarayya Abuja. Takardar mallakar gidajen na dauke da sunan gidauniyar  “Ariwabai Aruera Reachout Foundation” wadda Misis Jonathan na daya daga cikin jagororin gidaniyar.

Hukumar EFCC c eta shigar da kara a watan Satumba na shekarar 2018 inda ta nemi kotu ta zartasa da hukuncin wucin gadi na kwace gidajen saboda ana gudanar da binciken wasu laifuka da suka shafe su.

Da yake yanke hukunci jiya Litinin, mai shari’a Nnamdi Dimgba, ya ki amincewa da bukatar lauyan Misis Jonathan, na ayi watsi da bukatar EFCC saboda wai babu kwakwarar dalilin yin haka, kotun ta umurci kwace kaddarorin amma na tsawon kwanaki 45.

Mai shari’ar ya ce, dole hukumar EFCC ta gama binciken da za ta gudanar da kuma gabatar da wadanda suke da laifin dangane da kaddarorin a cikin kwanaki 45.

Ya kuma kara da cewa, hukumar EFCC nada hurumin neman karin wa’adi in basu kamala aikin su ba kafin wa’adin kwanaki 45 ya kare.

Ya kuma umurci cewar, duk lokacin da hukumar EFCC ke bukatar gudanar da wani aiki a cikin gidajen dole suyi haka tare da kasancewar bangaren lauyoyi ko wakilan Misis Patience Jonathan.

 

Exit mobile version