Ammar Muhammad" />

Kotu Ta Dage Shari’ar Nyako Kan Zargin Badakalar Naira Miliyan 29

Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, a yau Laraba ya da ge shari’ar tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako har zuwa 13 ga watan Mayu domin sake sauraren shaidun da lauya mai kare shi zai gabatarwa da kotun.

A lokacin da kotun ta kira lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya shaidawa kotun cewa; Kanu Agabi, SAN ya rubuta a wata takarda cewa ba zai sami damar halartar kotun ba.

Atolagbe, ya shaidawa kotun cewa; ya kamata shari’ar ya ci gaba gabatar da shaidunsu a kotun.

Sai dai mai kare shi Bart Ogah ya ce suna da bukatar karin lokaci domin yiwa takardun karatun ta natsu domin ba su damar yiwa shaidun tambayoyi.

Mai Shari’a Okon Abang ya da ge shari’ar har zuwa 13, 14, 15 ga watan Mayun 2019.

Nyako dai da ‘ya’yansa Abdulaziz Nyako, Abubakar Aliyu da Zulkifik Abba ana zarginsu ne da laifuffuka 37 wanda ya hada da na zambo cikin aminci, sata, da dai sauran su.

 

Exit mobile version