Kotu Ta Daure Dan A-Caba Shekara 4

Wata babban kotun majistiri da ke garin Minna a jihar Neja ta yanke ma wani dan A-caba mai suna Adamu Mohammed dan shekara 23 daurin shekaru hudu a gidan kirkiri a bisa kamasa da laifin yin luwadi da yara shida.

An gurfanar da Adamu Mohammed a bisa kamasa da laifin yin luwadi wanda ya saba wa doka ta sashi na 284 da ke karkashin Final Kod.

Dan sandan da ke gabatar da kara, ASP Daniel Ikwoche ya shaida wa kotun cewar wani mai suna Yusuf Buhari shine ya sanar da ofishinsu na Chanchaga rahoton aukuwar hakan a ranar 6 da watan Oktoba.

Ya ce; Mista Ikwoche ya kai korafinsa kan cewar wanda suke zargin ya yi luwadi da dansa mai shekaru 10 a cikin gidansa da ke kauyen Korokpa da ke garin Minna inda yake zarginsa da yin hakan sau da yawa.

Dan sandan ya shaida cewar da suka zafafa bincikensu ne har suka gano wanda suke zargin ya aikata wannan laifin har wa yara biyar dukkaninwasu wadanda suke kasa da shekaru 10 zuwa 12, inda ya shaida cewar dukkaninsu suna zaune ne a garin na Korokpa.

A lokacin da kotu ta karanta ma wanda ake zargin ‘Adamu Mohammed’ laifinsa, ya amince da laifin da aka zarginsa sai ya nemi kotun ta yi masa sassauci a cikin hukuncin da za ta yanke masa.

Dan sandan da ke shigar da kara, ya roki kotun da ta yanke hukunci ga wanda suke zargi daidai da laifin da ya aikata a karkashin sashi na 157 da ke karkashin manyan laifuka na ‘Criminal Procedure Code’.

A hukunsa da ya yake wa wanda ake zargin, Alkalin kotun Nasiru Mu’azu ya daure mai laifin shekaru hudu a gidan kaso, hadi da tabbatar da ba shi ayyukan azaba a rayuwarsa ta shekara hudun da zai shafe a gidan yari bisa wannan laifin na luwadi.

 

Exit mobile version