Kotu Ta Daure Matasa Biyu Saboda Satar Tinkiya A Yobe

Wata babbar kotun Majistare mai daraja ta 1 dake da zama a garin Damaturu cikin Jihar Yobe ta yanke hukuncin daurin watanni biyu ko zabin biyan tarar Naira dubu daya kowanensu ga wasu matasa biyu da aka samu da satar Tunkiya a unguwar cikin garin Damaturu.

Da ya ke bayani gaban kotun dan sanda mai gabatar da masu laifin Sufeto Moses Tunjini ya ce  sakamakon rahoton da wata mata mai suna Fatima Iliya da ke da zama a unguwar Nainawa cikin garin Damaturu ta kai ofishin su na ‘yan sanda tun a ranar 4 ga watan Oktoban shekarar 2017 matasan biyu da suka hada da Kabiru Mohammed dan shekaru 28 da kuma Samaila Abdullahi dan shekaru 17 sun sace mata Tunkiyarta da kudinta zai kai Naira dubu 15.

Don haka ne a cewar dan sanda mai gabatar da masu laifin ya ce wannan laifi da matasan suka aikata ya saba dokar shari’a ta penal code sashi na 97 da kuma sashi na 287.

Bayan da aka karanta musu laifin da suka aikata  matasan sun amince kana suka nuna nadamarsu da neman kotun ta musu sassauci ya yin yanke musu hukunci tare da daukar alkawarin za su gyara halinsu.

Da ta ke yanke hukuncin bayan da ta ji jawabin dan sanda mai gabatar da kara alkalin kotun mai shari’a Hasiya Abubakar  nan take ta yanke wa matasan daurin shekara daya ga kowanensu ko kuma zabin biyan tarar Naira dubu daya ga kowanensu bisa ga dogaro da sashi na 97 da 287 na

dokar ‘Penal Code’.

 

Exit mobile version