Connect with us

RAHOTANNI

Kotu Ta Daure Matashi Wata Shida Da Bulala Biyar Kan Satar Wayoyi

Published

on

Kotun Majistare da ke karamar hukumar Kafanchan a Jihar Kaduna ta daure wani matashi mai shekarun haihuwa 19 mai suna, Sunday Dabid, tsawon watanni shida da kuma bulala biyar a bisa samun sa da aikata laifin satar wayoyin hannu guda biyu da tsabar kudi naira 13,500.

Sai dai alkalin kotun Mista Abdulaziz Ibrahim, ya bai wa matashin zabin ya biya tarar naira 20,000.

Dabid ya amsa aikata laifinsa na shiga waje babu izini da kuma yin sata, wanda hakan ya saba wa sashe na 333 da na 271 na kundin aikata laifuka na Jihar Kaduna.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insifeka Johnson Ibudu, ya shaida wa kotun cewa wani ne mai suna Mista Sunday Hillary, ya kai karar hakan a ofishin ‘yan sanda a ranar 4 ga watan Afrilu.

Ibudu ya ce, wanda ya kai karar ya yi zargin cewa wani da bai san shi ba ya balle gidan wani mai suna Mista Anthony Diam, ya shiga ya yi satar wayoyi biyu kirar Tecno da Fero, da kuma tsabar kudi naira 13,500.

Ya ce a lokacin bincike, ‘yan sanda sun gano cewa Dabid ne ya aikata laifin.

Mai gabatar da karan ya roki kotun da ta hukunta Dabid kamar yanda sashe na 125(8) na kundin aikata laifuka ya tanada tun da ya amsa aikata laifin na shi.

 
Advertisement

labarai