Yusuf Shuaibu" />

Kotu Ta Daure Wanzami Shekara 20 Bisa Lalata Diyar Makwabciyarsa

Wata kotu ta musamman da ke garin Ikeja, ta yanke wa wani wanzami mai suna Jobi Kayode, hukuncin shekara 20 a gidan yari, bisa laifin yi wa diyar makwabciyarsa mai shekara 12 fyade. Alkali mai shari’a Oluwatoyin Taiwo shi ya yanke wa Kayode wannan hukunci a ranar Juma’a, bayan ya same shi da laifin da a ke tuhumar sa da shi na yin fyade, sakamakon shaidu da a ka samu daga gwan da a ka yi wa yarinyar. “Yin fyade ya zama ruwan dare a cikin al’ummarmu, inda a yanzu haka ya zama wata annoba a cikin al’umma. Ka yi wa diyar makwabciyarka wacce ta yarda da kai mai shekara 12 fyade. “Kotu ta yanke wa wanda a ke tuhuma hukuncin daurin shekara 20 a gidan yarin Kirikiri ba tare da biyan wani tara ba. Hukuncin zai fara ne tun daga ranar 8 ga watan Nuwambar shekarar 2019,” in ji alkali mai shari’a.

A wannan shara’ar dai, masu gabatar da kara su gabatar wa kotu shaidu guda biyar wadanda su ka hada da na yarinyar, iyayenta, rahoto daga wajen likita da kuma na ‘yan sanda, wanda Kayode ya gamsu da su. Ita dai yarinyar ta na daliba ce a aji dayan sakandar, ta bayyana cewa, wanda a ke tuhumar ya na jan ta dakinsa a duk lokacin da ta dawo daga makaranta, inda ya key i lalata da ita. Ta kara da cewa, wata rana ta na kokarin shiga kofar gidansu, sai ta hadu da wannan mutumin inda ya bayyana mata cewa, ya na son ganin makwabciyarsu da ke cikin gidan. Ta cigaba da cewa, lokacin da ya shiga gidan, sai ya danne ta da karfi, inda ya yi mata fyade. “Ya yi min barazanar zai kashe ni idan ya fada wa wani abinda ya yi min,” in ji ta.

Yarinyar ta cigaba da cewa, ta ba ta fada wa wani abinda ya faru ba, bayan kwanaki uku sai ya kara mata fyade. Ta ce, ba ta fada wa iyayenta faruwar lamarin ba, amma dai ta fada wa wata kungiya faruwar lamarin lokacin da su ka zo ilmantar da dalibai yadda a ke yin jima’i a makarantarsu.

Da ya ke kare kansa, Kayode ya musanta yin lalata da diyar makwabciyarsa. “A wannan lokaci da ta ke magana na je gidansu ne domin ganin makwabciyarsu da ke cikin gidan. A ko da yaushe kofar shiga gidan ya na kulle,” in ji shi.

 

Exit mobile version