A ranar Laraba ce, kotun Benin ta yanke wa wani mutum mai suna Osas Iserhienrien dan shekara 39, hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari, bisa samun sa da laifin lalata itatuwan da kudinsu ya kai na naira miliyan daya. Alkali mai shari’a Patricia Igho-Braimoh ya yanke wa Iserhienien hukunci ne bayan da same shi da laifukan da a ke tuhuma sa da shi na lalata itatuwan tattalin arziki, wanda ya bukaci kotu ta yanke masa hukunci mai sassauci. Duk da haka dai, alkali mai shari’a Braimoh, ya bai wa wanda a ke tuhuma biyan tara na naira N250,000.
Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara Osayomwanbor Omoruyi, ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifin ne a ranar 29 ga watan Satumbar shekarar 2015, a kan titin Osayande da ke yankin Igue-Iheya cikin gundumar Egor a garin Benin. Omoruyi ya kara da cewa, wanda a ke tuhuma ya lalata itatuwan tattalin arziki mallakar wani mutum mai suna Mista Joseph Kubeyinje. Ya ce, itatuwan tattalin arzikin dai sun kai na naira miliyan daya. Haka kuma lauyan ya kara da cewa, wannan laifi ne da ya saba wa sashe na 451 da 332 da 81 da kuma na 252, wanda hukunci sa ke sashe na 351 da 1 (2) na dokar manyen laifuka mai lamba Cap. 48 Bol. 11 ta Jihar Edo ta shekarar 1976.