Yusuf Shuaibu" />

Kotu Ta Garkame Tsohuwa Mai Shekara 75 Da Danta Ya Gudu Bayan Bayar Da Belinsa

Makwabta tare da ‘yan’uwar Elizabeth Otubambo ‘yar shekara 75, sun nuna rashin jin dadinsu game da garkame ta da aka a gidan yari tun watar da ta gabata. An garkame Otunbambo ne a gidan yarin Ibara da ke garin Abeokuta cikin Jihar Ogun, bisa laifin da danta ya aikata.
Kamfanin dillancin labarai ta kasa ya ruwaito a garin Abeokuta ranar Juma’a cewa, tun ranar 15 ga watan Fabrairu aka garkamee Otumbabo, domin ta kasa bayyana danta mai suna Destiny Otubambo, wanda ya gudu bayan da aka ba da belisa, wanda mahaifiyarsa ta tsaya masa.
Tsohuwar tana zaune ne a garin Iyana Isashi da ke Ojo kusa da Jihar Legas, an bayyana cewa dama can tana fama da rashin lafiya, amma abin ya kara kamari ne lakacin da aka garkame ta a gidan yari.
Wata makwabciyar Otubambo mai suna Misis Bidemi Erinle, ta bukaci gwamnatin Jihar Ogun da ta shiga cikin lamarin domin a tabbatar da cewa tsohowar ba ta mutu a gidan yari ba. “Garkame tsohuwa ‘yar shekara 75, bisa laifin da danta ya aikata ya sabawa hakkin Dan’adam,” in ji Erinle.
Ta ce, tana kira da a saki Otubambo nan take, yayin da ‘yan sanda su ci gaba da neman danta.
Da yake magana kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun Mista Abimbola Oyeyemi, ya bayyana wa manema labarai cewa, an cafke Elizabeth ne bisa umurnin kotun Jihar Ogun. Ya kara da cewa, ‘yan sanda su cafke danta, bayan rahoton da mai otal din ‘Soultrag Hotel’ da ke kan titin Petetdo cikin garin Agbara ta Jihar Ogun, bisa rashin biyarsa kudin otal. Kakakin ‘yan sandar ya ce, Destiny ya kwana a otal tare da abokanansa guda uku na tsawan wata, inda aka lissafa kudin kusan naira miliyan daya. Oyeyemi ya bayyana cewa, an daure Destiny a gidan yari bayan an gurfanar da shi, daga baya an bayar da belin sa bayan mahaifiyarsa ta tsaya masa. Ya ce, kotu ta bayar da umurnin a garkame tsohuwar a gidan yari har sai an samu danta, domin ya fuskanci tuhumar da ake yi masa.

Exit mobile version