Connect with us

KASASHEN WAJE

Kotu Ta Haramta Shiga Yajin Aiki A Kasar Benin

Published

on

Kotun tsarin mulkin kasar Benin ta ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na haramta wa ma’aikatan kiwon lafiya da na ma’aikatun shari’a da kuma jami’an tsaron kasar shiga yajin aiki bai saba wa dokokin tsarin mulkin kasar ba.
Wannan hukunci da kotun tsarin mulkin kasar ta Benin ta bayyana ya kawo karshen takun sakar da aka share watanni da dama ana yi tsakanin bangaren zartarwa da hukumar shari’a ta kasar wacce ta bayyana dokar haramcin yajin aiki da majalisar dokokin kasar ta sanya wa hannu a watan Janerun da ya gabata a matsayin wacce ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
A hukuncin da ta bayyana kan wannan batu dai kotun tsarin mulkin kasar ta Benin ta ce ya zamo dole ga jami’an tsaro da na kiwon lafiya da su gudanar da aikinsu ala kullin halin kuma ba su da izinin shiga yajin aiki kuma ba bu hujja daya da za iya dogaro da ita domin dakatar da aikin kiwon lafiya da na tsaro a kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: