Mai shari’a Saliu Saidu na babban kotun tarayya dake yankin Legas ya zartar da hukuncin cewa Hukumar nan mai tasrifin kaddarori ta kasa AMCON ta karbe gudanar da kanfanin sarrafa abinci ta “Osigwe Foods and Agro Industrial Company Limited” wanda mallakin Cif Anselm Kayode Mohammed ne, bayan da Hukumar AMCON ta shigar da karar neman yin haka.
Hukumar AMCON na bin kanfanin sarrafa abincin Naira Biliyan 5 wanda ita ma ta shiga tsakanin kanfanin ne a kan wasu kudade da suka fito ta Union Bank da Unity Bank da Ecobank da kuma rusashiyar FinBank.
Hukuncin ya kuma hada da gidan shugaban kanfanin dake lamba17, Sowemimo Street, Ikeja GRA, a jihar Legas, wanda bayan shi da iyalisa har da ‘yan haya a cikin gidan, kamar dai yadda sanarwar da aka fitar ranar Litinin ta nuna.
Tuni dai Hukumar AMCON ta nada Cif Robert Ohuoba a natsayin wanda zai kula da harkokin gudanarwar kanfanin na Osigwe Foods and Agro Industrial Company Limited dake Iju Gudugba Billage kan hanyar Agege Iju Waterworks a karamar hukumar Ifako-Ijaiye ta jihar Legas.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa, “Dokan ya fara aiki ne a dai-dai karfe 2;30 na ranar Talata 19 ga watan Fabrairu 2018, in da za a mallaki gidan Cif Anselm Kayode Mohammed da kuma kanfanin Osigwe Foods and Agro Industrial Company Limited”
“Mai shari’a Saidu, ya anince da nada Cif Robert Ohuoba domin ya zama mai lura da harkokin kasuwanci da kaddarorin kanfanin Osigwe Foods and Agro Industrial Company Limited a duk inda suke matukar suna yankin da kotun nan ke da iko. Matukar kaddarorin na kanfanin “Osigwe Foods and Agro Industrial Company Limited” ko kuma na mai kanfanin Cif Anselm Kayode Mohammed ne.”
Kotun ta umurci Shugaban ‘yansanda na kasa da kwamishinonin ‘yansanda na jihohin tarayyar kasar nan da su taimaka wa ma’aikacin kotun wajen tabbatar da wannan dokan, dai-dai da sashi na 4 na dokokin ‘yansanda da sashi na 287 (3) na kudin tsarin mulkin kasar nan.