Kotu Ta Soke Zaben Alasan Ado Doguwa Na Jam’iyyar APC

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna yau Litinin ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Tudun Wada/Doguwa, wato Alasan Ado Doguwa. Alasan Ado Doguwa wanda shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya wato mai mukami na uku a majalisar bayan shugaban majalisar da mataimakinsa.

Kotun har wala yau ta ce ta soke zaben da ya kawo Alhassan Doguwa a matsayin dan majalisa a kananan hukumomi biyu. Inda kotun ta bayyana zaben a matsayin mara inganci.

Mai shari’a Justice Oludotun Adefope-Okojie, ya ce bayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zabe ba zai yiwu ba, domin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta cire sunayen wadansu jam’iyyun a yayin ayyana sakamakon zaben.

Har wala yau kotun ta ce INEC ta karya doka ta hanyar rubuta sakamakon zaben jam’iyya biyu kawai cikin 53 da suka shiga zaben a fom mai lamba 0EC 8 (II) E. A don haka kotu ta nemi INEC ta sake shirya wani zaben nan da kwana 90 a yankin.

Exit mobile version