Wata kotun Majistare da ke zamanta a Osogbo, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare mutum biyu, Saliu Saheed da Azees Rafiu bisa zargin satar buhun masara 18 da kaji 1032. Mai gabatar da kara, Jacob Akintunde, ya fadawa kotu cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2021, a gonar Oyebode da ke kauyen Abudo, Ede, Jihar Osun.
Ya fadawa kotu cewa Rafiu, lokacin da mai gidan ba ya kusa ya gayyaci wanda ake kara na 1, Saheed, wanda aka kore shi daga aikin kiwo a wurin. Mai gabatar da kara ya cigaba da cewa an gano buhunan masarar da aka sace a gidan wadanda ake tuhumar.
Ya ce wanda ake tuhuma na farko direba ne a kamfanin, yayin da wanda ake kara na biyu ma’aikaci ne a bangaren kula da da kaji. A cewar takardar cajin, laifin ya sabawa sashe na 516,39 (9) na kundin laifuka mai lamba Cap 34 bol 2 na Jihar Osun, 2003. A halin yanzu, wadanda ake tuhumar sun amsa laifin da kotu ta tuhume su da ‘yan sanda.
Mutanen biyu sun fadawa Kotu cewa sun sace buhun masara hudu ne kawai daga wurin kajin kuma ba su da masaniya game da kajin da aka ce sun sace. Lauyan da ke kare wanda ake kara, Olatunbosun Oladipupo ya lura cewa mai gabatar da kara ya tabbatar da gaskiyarsa, yayin da wanda ake kara ya yi musu cewa sun sace masarar ba kaji ba. Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Ishola Omisade, ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a Cibiyar Gyara ta Ile-Ife. Alkalin Kotun, ya dage sauraron karar zuwa 16 ga Maris, 2021, don ci gaba da sauraro.