Umar Faruk" />

Kotu Ta Tsare Matar Da Ake Zargi Da Sace Jariri A Kebbi

Kotu

A jiya ne kotun majistare mai lamba 4 da ke zamanta a Birnin-Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, a karkashin Majistare Zainab Bello Suru, ta bada umarnin cigaba da tsare Patricia Nebochi a gidan gyaran hali da ke Argungu, bayan da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar suka cafke su ka gurfanar da ita a gaban kotun bisa tuhumar ta da aikata laifufuka biyu; laifin sace jaririn da a ka haifa a ranar 21 ga Nuwamba, 2020, da misalin karfe 4:00 na yamma a asibitin Aisha Muhammadu Buhari da ke garin Jage da kuma laifin zama sanadiyar mutuwar jaririn ta hanyar wurgar da shi.

Alkalin ta ce, za a cigaba da tsare matar ne har zuwa lokacin da za a cigaba da gabatar da shari’ar a sabuwar shekara karkashin wata babbar kotu a jihar, wacce ke da cikakken hurumin sauraron shari’ar, saboda kasancewar laifin da a ke tuhumar Patrichia, babba ne.

Jami’in ‘yan sanda mai gabatar da karar, Sufeto Muktari Mati, ya bayyana wa Mai Shari’ar Zainab Suru cewa, “ni Sufeto Muktari Mati a madadin rundunar ‘yan sandan jihar ne ke gabatar da Patricia Nebochi, ‘yar shekaru 30 da haifuwa, wacce ke zaune a garin Tambuwal a Jihar Sakkwato, a gaban wannan kotun da laifufuka biyu.

“Laifi na farko; tuhumar ta da sace jariri sabuwar haihuwa, sai laifi na biyu na zama sanadiyyar mutuwar jaririn da wata mata mai suna Fatima Ja’afar da ke garin Galbi a karamar hukumar mulki ta Jega, wanda ya saba wa sashe na 221 da kuma na 274 na kundin tsarin hukunta masu laifi, wato Panel Cod).”

Bisa ga hakan, Mai Shari’a Zainab Bello Suru ta bada umarnin a karanta wa matar da a ke tuhuma a gaban kotu da sace jariri da kuma laifin kisa ta hanyar zama sanadiyar mutuwarsa laifufuka biyu da aka gabatar da ita akansu, inda bayan Rijistaran kotun ya kammala karanta laifufuka da a ke tuhumar ta da su, sai Patricia Nebochi ta musanta tuhumar ta a ke yi ma ta a gaban kotun.

Daga nan Sufeto Mati ya nemi kotun da ta dage sauraren karar har zuwa ranar 5 ga Janairu, 2021, domin bai wa rundunar ‘yan sandan damar kammala duk binciken da su ke gudanarwa, don a dawo a ciki gaba da sauraron karar.

Bugu da kari maishari’a Zainab Bello Suru ta amince da rokon na mai gabatar da karar. Haka kuma ta bada umarnin tsare wacce a ke tuhuma a gidan gyaran hali da ke Argungu har zuwa ranar zaman shari’ar.

Sai dai kuma alkalin ta ce, wannan kotun ba ta da hurumin cigaba da sauraron karar. Don haka sai dai a jira shawarar Darakta Mai Kula da Gurfanar da Manyan Laifuka na Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kebbi, wato DPP.

Exit mobile version