Idris Aliyu Daudawa" />

Kotu Ta Tsare Mutum Saboda Zina Da ‘Yar Shekara Sha Hudu

Makanike

Ranar Jumma’a ce babban majistare na kotun dake Osogbo jihar Osun ya bayar da umarni na tsare wani mutum dan shekara 44 mai suna Kazeem Olapade a gidan gyara halin ka na Ilesa, saboda kamata shi da aka yi da laifin yin zina da budurwa mai shekara goma sha hudu.
Manema labarai sun bada rahoton cewar shi Olapade ya na fuskantar aikata laifuka uku da suka hada da cin mutunci, fyade, da kuma lalata da wata budurwa. Sai dai kuma shi wanda ake zargin da aikata laifukan ya ki amincewa.
Majistare Dokta Olusegun Ayilara ya bada umarnin a cigaba da tsare shi mai laifina gidan gyara halinka, saboda karfin laifin daya aikata.
Ayilara sai ya fadi maganar data zarce karfin shi neman wanda ke kare shi Mista Jimmy Jones ya yi, maimakon haka ma sai aka dage sauraren ita karar inda aka sa wata rana.
An dai dage sauraren karar har zuwa 5 ga watan Fabrairu inda za a tattauna akan cancantar bayar da belin.
Mai gabatar da masu laifi Insfekta Jacob Akintunde ya shaidawa kotun cewar shi mutumin ake zargi da aikata laifin cewar ya aikata laifukan ne tsakanin 22 ga watannin Agusta shekarar data gabata, da kuma Janairu 2021 a Osogbo.
Akintunde ya bayyana cewar shi mutumin da ake zargin ya yi lalata da budurwar, ba tare da amincewar ta ba, wadda kuma ba a bayyana sunanta ba.
Amma daga baya sai yarinyar ta bayyana abinda yake faruwa, wanda kuma hakan ne yasa aka kama shi wanda ake zargin, aka kuma gurfanar da shi a gaban Kotu.
Kamar dai yadda ya bayyana shi aikata laifin ya sabawa dokar sassa na 31 (1) na dokar bata kananan yara a jihar Osun, shekarar 2007(2) na 2007 , da kuma sassanan 214(1) da 360 na dokar aikata laifi na Cap. 34, bol. 11, dokokin jihar Osun shekarar 2002.

Exit mobile version