Kotu Ta Umarci Kulle Wasu Mutane 8 Saboda Tayar Da Hankalin Jama’a A Osun

Daga Bello Hamza,

Wata kotun majastare da ke garin Ile-Ife ta jihar Osun ta umarci wasu mutane 8 da ake tuhuma da karya doka da kuma tayar da hankalin al’umma.

Mutane 8 da ake tuhuma sun hada da, Felicia Hammed, 51; Taye Hamzat, 25; Olarewaju Adebayo, 20; Sule Hammed, 45; Famadewa Adeniran, 23; Adetoye Adelowo, 27; Samson Ojo, 34 da kuma John Micheal, 26.

Mai gabatar da karar, Asp. Adebayo Joseph, ya bayyana wa kotun cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Fabrairu da misalin karfe 10 a yankin Enuwa na garin Ile-Ife.

Adebayo ya ce, sun hada baki ne wajen aikata laifin ta hanyar gangami inda suka aikata laifin tayar da hankalin jama’a tare da barazana ga zaman lafiyar al’umma.

Ya kuma kara da cewa, gangamin mutane ya tayar da hankalin al’ummar yankin, ya kuma ce, laifin ya saba wa sashi na 70, 249 (d) da 517 na dokar manyan laifuffaka na jihar Osun na shekarar 2002.

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.

Daga nan ne lauyan Wadanda ake zargin, Mr Philip Fasanmoye, ya bukaci a bayar da belin su, kamar yadda doka ta tanada.

Alkalin kotun A. A. Adebayo ya ki amincewa da bukatar bayar da belin inda ya umarci a wuce da su gidan yarin garin Ilesa, ya ce hakan zai zama darasi da masu hankoron aikata irin wannan laifin a nan gaba.

Alkali Adebayo ya kuma daga karar zuwa ranar 22 ga watan Maris don sauraron shaidu.

Exit mobile version