Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci tsohon shugaban kwamitin farfado da tara kudade fansho, Abdrulrasheed Maina da ya fara gabatar da jawaban kariyan kansa gami da shaidun da za su kareshi kan zarge-zargen da ake masa daga ranar 26 ga watan Janairun zuwa 27 na 2021.
A jiya ne Alkalin kotun, Okon Abang ya ce Maina na iya kiran shaidunsa su 21 da ya nuna cewa yana da su da za su kareshi domin su zo gaban kotun don yin bayanin su.
A dai ranar 25 ga watan Oktoban 2019 ne EFCC suka gudanar da Maina a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda 12 tare da dansa Faisal da shi kuma ake masa tuhume-tuhume guda uku da suka jibinci mu’amala da kudade ba bisa ka’ida ba tare da zargin badalakar kudade.
Dukkaninsu an bayar da belinsu, inda Sanata Ndume ya tsaya wa Maina wajen belinsa.
Jami’an tsaro sun kai ga kamo Maina ne a jamhuriyyar Nijar a ranar 4 ga watan Disamban 2020.
A zaman da kotun ta yi na karshe dai Maina ya yanki jiki ya fadi a gaban kotun, lamarin da ya sanya kotun dage zamanta ba tare da shirin hakan ba.