Daga Khalid Idris Doya
Babban Kotun tarayya da ke Abuja ta bai wa shugaban tundunar ‘yan sandan
Nijeriya da wasu mutum biyu da su gurfanar da wani dan kasuwa mai suna Chika
Ikenga da kamfaninsa mai suna Eunisell Chemicals Limited, bisa zargin
shafi fitar da jabu da wasu zarge-zarge.
Har ila yau, an umarnin ya kuma shafi mataimakin Sufeta Janar DIG
Michael Anthony Ogbizim na sashin kula da manyan laifuka da bincike
(FCID) da kuma mataimakin kwamshina (DCP) Augustine Sanomi, wanda kuma
shine kwamishinan ‘yan sanda a bangaren shari’a na FCID.
Justice Taiwo Taiwo shine ya bada wannan hukunnin a kan kara mai
lamba: FHC/ABJ/CS/1580/2019 wanda Kenneth Amadi, Hapiness Amadi da
Idip Nigeria Limited da wasu suka shigar, su na neman umurnin da zai
kai ga tilasta ma wadanda ake kara da su sake gurfana kan karar da
‘yan sanda suka shigar da fari a kan Ikenga, Surajo Yakubu da Eunisell
Chemicals, wanda ‘yan sanda suka janye karar daga baya.
A hukuncin da ya yanke a ranar 16 ga Nuwamba wanda aka fitar da
kwafinta a ranar 25 ga Nuwamba, ya shaida cewar a bisa dogara da
hujjoji da bayanan da suke gabansa don haka ya amince da bukatar masu
shigar da kara na neman a sake gurfanar da wadanda ake tuhumar domin
ci gaba da sauraron shari’ar.