Kotu Ta Umurci DSS Ta Biya Diyyar Miliyan 10 A Bisa Harbin Wani Mutum Ba Bisa Ka’ida Ba

Babban Kotun Tarayya da ke Bauchi, a ranar Juma’ar nan da ta gabata ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da ta hanzarta biyan tsabar kudi har naira Miliyan goma 10 ga Musa Ibrahim Umar da ke zaune a layin Iyamadu a karamar hukumar Bukuru da ke jihar Filato-Jos a matsayin kudin diyyar harbinsa da suka yi.

Wannan hukuncin na zuwa ne biyo bayan kewaye masa gida da kuma bude masa ruwan alburusai ba bisa ka’ida ba; wadda har ta kai sun lalata masa guiwarsa a wani lokaci a cikin shekara ta 2016.

Wakilinmu ya labarto cewar, lamarin ya samo asali ne a lokacin da DSS suke tsaka da gudanar da binciken wani da suke kyautata zaton dan Boko Haram ne mai suna Umar Khalid Muhammaed, a yayin binciken nasu sun yi kokarin shiga unguwar a ranar 2 ga watan March na 2016 a bisa kuskure kuma suka fada gidan wadda suka tarwatsa masa guiwar da tsammanin shi ne suke nema a tsakar daren ranar da suka kaddamar da binciken neman dan babu bokon.

Daga bisani ne kuma DSS din suka tabbatar da cewar tabbas wadda suka kai masa harin wato Musa Ibrahim Umar ba shi ne suke nema ba; inda suka farmaki Musa wadda har ta kai sun zubda masa da jininsa a cikin rashin sani.

Wadanda suke gabatar da karan sun bayyana cewar wannan lamarin take hakkin dan adamtaka ne daga bangaren jami’an tsaro, inda suka dogara da sashi na 33 da ke kundin tsarin 1999 wadda aka yi wa kwaskwarima cewar hakan an shiga hakkin wadda tsautsayin ya rufta masa.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mai shari’a Muhammad Shitu Abubakar ya bukaci wadanda ake karan wato hukumar DSS da su biya wadda ke kara zunzurutun kudi har naira miliyan goma (10 milion) domin ya samu dan rage radadin abun da suka aikata masa ba bisa ka’ida ba. a matsayin kudin diyyar harbisa.

Haka kuma, Alkalin ya bukaci hukumar ta baiwa wadda ta yi wa wannan aikin hakuri ta hanyar wallafa ban hakurin a cikin manyan jaridun da suke kareda kasar nan guda biyu.

Lauyan wadda ya shigar da kara, Barista Akibu Idris esk, ya gode wa kotun a bisa wannan hukunci na adalci da ta yanke, yana mai bayyana cewar wannan hukuncin shi ne ya dace daidai da laifin da aka aikata musu, ya kuma yi bayanin cewar shari’a ita ce gatar dukkanin wadda bai da galihu a cikin al’umma.

Lauyan kariya, Barister B. A Joshua wadda ya samu wakilcin Barrister Imam a yayin zaman yanke hukuncin.

 

Exit mobile version