Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta wanke tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, daga tuhumar zambar kuɗi Naira biliyan 3.3.
Mai shari’a Chukwujekwu Aneke, ya yanke hukuncin cewa hukumar EFCC ba ta gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da laifin Fayose ba.
- Yara 2 Sun Kuɓuta Bayan Shafe Shekaru 6 A Hannun Boko Haram A Borno
- EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari
Alƙalin, ya ce shaidun da EFCC ta kawo da takardun da aka gabatar ba su nuna Fayose ya aikata laifin ba.
Don haka, kotun ta amince da buƙatar Fayose na cewa babu hujja a kansa, kuma ta wanke shi daga duka tuhume-tuhume 11.
EFCC, ta zargi Fayose da karɓar Naira biliyan 1.8 daga hannun tsohon Ministan Tsaron Cikin Gida, Sanata Musiliu Obanikoro, ba ta hanyar amfani da banki ba.
Haka kuma, ta ce ya sayi kadarori a Legas da Abuja da kuɗaɗen da ake zargi na haram ne, sannan ya adana wasu maƙudan kuɗaɗe a asusun bankin kamfanoni da danginsa.
Fayose, ya musanta dukkanin waɗanda tuhume-tuhumen, inda ya ce kuɗin da ya karɓa na halal ne kuma ya yi amfani da su bisa doka.
Lauyoyinsa sun ce shari’ar tana da nasaba da siyasa kuma babu wata ƙwaƙƙwarar hujja a kanta.
Magoya bayan Fayose sun bayyana jin daɗinsu kan hukuncin, inda suka bayyana cewa an samu nasarar yin adalci.
EFCC dai ba ta bayyana ko za ta ɗaukaka ƙara ba tukuna.